Daga USMAN KAROFI
Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta zargi shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da hukunta ta saboda ta ƙi amincewa da buƙatarsa na yin hulɗa da ita. Sanatar ta bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da ita a Arise TV, inda ta ce lamarin ya faru a lokacin da take gidan Akpabio a Uyo don bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
Ta bayyana cewa yayin da take zagayawa da Akpabio a gidansa, sai ya tambaye ta ko tana son gidan, inda ta amsa da cewa, “Eh, sir, gida ne mai kyau.” Sai ya ce mata, “Yanzu da kin zama Sanata, ina so ki zo nan a duk lokacin da kike da dama domin mu huta.” Ta ce hakan ya nuna yana da wata manufa a zuciyarsa, kuma tun daga lokacin ya fara nuna mata wariya a majalisa.
A makon da ya gabata, Natasha ta tayar da rikici a zauren majalisa lokacin da ta ƙi amincewa da kujerar da aka bata, inda ta dage kan batunta duk da umarnin Akpabio. Daga bisani, majalisar ta tura lamarin zuwa kwamitin ladabtarwa domin a duba batun. Sai dai sanatar ta nemi a gudanar da binciken a fili, ba a bayan fage ba.
A wani mataki na kare kanta, Natasha Akpoti ta maka Akpabio da wani hadiminsa, Mfon Patrick, a kotu, tana neman diyyar naira biliyan ɗari bisa zargin ɓata mata suna. Ta buƙaci kotu da ta umarci su janye kalaman da suka yi tare da bayar da haƙuri a jaridar ƙasa. Wannan batu ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da al’ummar Najeriya.
