NBC ta kafa wa tashoshi 25 takunkumi kan saɓa ƙa’idar aiki

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Tashoshin Talabijin da Rediyo (NBC), ta bayyana cewa ta kafa wa wasu tashoshin yaɗa labarai 25 takunkumi yayin zaɓen Shugaban Ƙasa da na majalisun tarayya da ya gudana.

Kazalika, ta ce, ta bai wa su kafofi 16 gargaɗin ƙarshe kan su kula da yadda suke gudanar da harkokinsu in ba haka ba su ma su fuskanci takunkumi.

Shugaban NBC, Balarabe Ilelah, ya ce hukumar ta ɗauki matakin kafa wa tashoshin takunkumi ne bayan da aka same su da saɓa ƙai’dar aiki a lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gudana.

Balarabe ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya shirya ranar Laraba a Abuja.

NBC ta ce wajibi ne kafofin yaɗa labarai su yi biyayya ga dokokin watsa labarai da kuma Dokar Zaɓe da makamantansu waɗanda suka shimfiɗa ƙa’idojin yadda za a yaɗa harkokin zaɓuɓɓukan 2023.

Da yake jawabi, shugaban NBC ya jaddada buƙatar da ke akwai kafafen watsa labarai su zamo masu kiyaye dokokin aiki yadda ya kamata.

Ya ce, an kafa wa ɗaya daga cikin tashoshin da lamarin ya shafa tukunkumi ne bisa yin riga-malam-madallaci wajen sanar da sakamakon zaɓe tun kafin hukumar zaɓe, INEC.

Wanda a cewarsa, hakan laifi ne da ya saɓa wa Sashe na 5.33 na Kundin dokokin NBC.