NCDC ta fitar da sanarwa kan zargin cutar Ebola a Abuja

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Hukumar NCDC ta ƙasa ta bayyana cewa an yi gwaji kan mutum biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar Ebola da Marburg a Abuja, amma sakamakon ya nuna cewa babu wanda ya kamu da cututtukan.

Hukumar ta ce, duk da haka, ana ci gaba da gudanar da bincike kan wasu cututtukan zazzaɓin j Lassa da dengue. Shugaban NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a domin kwantar da hankulan jama’a bisa raɗe-raɗin ɓullar cutar Ebola a babban birnin tarayya.

Daga cikin waɗanda aka yi wa gwaji akwai wani matafiyi da ya dawo daga Kigali, ƙasar Rwanda, wanda ya garzaya asibiti bayan ya fara jin alamomin rashin lafiya.

NCDC ta yaba da wannan mataki da ta kira abin koyi ga sauran ‘yan ƙasa, tare da godewa likitoci da jami’an asibitin Nisa Premier da suka hanzarta kai rahoto, lamarin da ya sa aka ɗauki matakan gaggawa da suka rage barazanar yaɗuwar cutar. Hukumar ta kuma godewa tawagar sa ido ta Abuja, Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta FCT, da sauran hukumomi da suka haɗa kai wajen daƙile fargabar ɓarkewar cuta.

NCDC ta tabbatar wa al’umma cewa babu ɓullar cutar Ebola a Najeriya, amma ta ƙara matakan sanga idanu saboda ɓarkewar cutar a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo. Matakan sun haɗa da ƙarfafa sa ido a filayen jiragen sama, tashoshin ruwa da iyakoki, tanadin wuraren killace masu cuta da kayan kariya, da kuma shirya gwaje-gwaje da horo a faɗin jihohi.

An kuma shawarci jama’a su kiyaye tsaftar jiki, gujewa hulɗa da namun daji ko naman da ba a san asali ba, tare da garzayawa asibiti idan sun fuskanci alamomin zazzaɓi, ciwon kai, ciwon makogwaro ko gajiya bayan tafiya.

By ukarofi