NDE ta horar da mutane 20,000 sana’o’i daban-daban a Bauchi

Daga MUAZU HARƊAWA a Bauchi

Hukumar samar da aikin yi ta ƙasa wato National Directorate of Employment ta horas da mutane dubu 20 a fannonin koyon sana’a daban-daban a jihar Bauchi.

Hukumar ta NDE ta gudanar da bikin yaye ɗalibai sama da ɗari shida daga cikin dubu da aka horas a ƙaramar hukumar Bauchi, inda aka gudanar a harabar ofishin da ke Bauchi.

Alhaji Aliyu Lawan Yaya shi ne Daraktan hukumar NDE a jihar Bauchi, inda ya ce daga Abuja an bayar da gurabai dubu 20 wa jihar Bauchi, inda a kowace ƙaramar hukuma aka horas da mutane dubu ɗaya. Ana ba su alawus na Naira dubu 20 na tsawon watanni uku, kowa ya samu dubu sittin.

Aliyu Lawal Yaya ya ƙara da cewa amma saboda a samu ci gaba yawanci sun haɗa kuɗi kowane ɗalibi ya bada dubu goma sun haɗa sun sayi shanu sun ɗaure, sai sun yi tsada su sayar, wannan tsarin ya taimaka sosai a haɗaka ta gamayya.

Aikin ya gudana a ƙarƙashin wani shiri na SPU inda ɗaliban suka yaba sosai. Abubakar Sani ya bayyana cewa ya samu Naira dubu sittin amma ya ci gaba da sayen dabbobi, a yanzu haka sun kai Naira dubu 160, sakamakon sayen ƙananan dabbobi huɗu yana kiwatawa idan sun girma ya sayar. Ya ce da haka ya ci moriyar horon da ya samu na wata uku da ake ba su dubu 20 kowane wata.

Ita ma wata ɗaliba da ta ci moriyar shirin mai suna Maimuna Sani Jibrin unguwar sarakuna  ta yaba game da samun kanta cikin shirin, inda ta ce ta samu dubu 60 ta zuba kaji 30, yanzu sun zama guda 160 cikin lokacin da ta fara kiwon kajin.

Shi ma wani ɗalibi Surajo Umar ya ce a baya shi tela ne, ya shiga shirin da wannan kuɗi dubu 60 ya fara sayo yadi yana sayarwa, inda yanzu kasuwancin sa ya haɓaka yana neman ficewa daga ɗinki zuwa saye da sayarwar tufafi.

Jami’i mai sa ido daga ofishin hukumar NDE a Abuja kuma Darakta kan ƙananan masana’antu, Mista Apochi Uba Mathew ya bayyana cewa wannan shiri na horaswa yana tafiya daidai, kuma sun samar da littafai guda tara kan koyar da sana’a nau’i daban-daban, kana an samu nasara kan shirin.