
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), ta ce ta na shirin gudanar da bincike game matsalar ɗaukewar lantarki da ake samu a ƴan kwanakin nan daga rumbun lantarkin Nijeriya.
Ta ce dalilin yin hakan shine don gano ainihin musabbabin abin da ke haifar da faruwar lamarin akai-akai.
NERC ta bayyana hakan ne ta shafinta na X a ranar Asabar inda ta ce za a yi hakan ne don samar da mafita ta dindindin game da al’amarin.
Hukumar ta kuma ce za ta sanar da rana da lokaci da za a yi zama game batun wanda ake fatan masu-ruwa-da-tsaki su hallara don samun nagartaccen sakamako.
Lamarin dai ya kan shafi jihohi da dama ciki har da babban birnin tarayya Abuja wanda ke haifar da koma baya ga harkokin al’umma na yau da kullum.
