
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe ya miƙa saƙon ta’aziya da jaje ga al’umma da gwamnatin Jihar Jigawa bisa mummunar iftila’in gobarar motar man fetur da ta yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.
Mataimakin gwamnan ya kuma sanar da bada tallafin kudi Naira miliyan 50 ga gwamnatin jihar don rage raɗaɗi ga iyalan mutanen da suka mutu da waɗanda suka jikkata .
Da ya ke jawabi bayan ya karɓar tallafin kuɗin, gwamnan Jigawa, Alhaji Umar Namadi ya yi godiya ga gwamnatin Katsina bisa turo tawaga ta musamman domin yin jaje tare da bada tallafin kuɗin.
Gwamnan ya kuma yi tsokaci game da kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya bayyana a matsayin abin da ya wuce harkar gwamnati zuwa na ƴan’uwantaka.
