Ƙaramar hukumar Anka za ta wakilci Jihar Zamfara a matakin wasan ƙwallon ƙafa na hukumar UBEC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar bada ilimin bai ɗaya reshen Jihar Zamfara (ZSUBEB) da haɗin gwiwa da hukumar ta ƙasa (UBEC) sun gudanar da wasan ƙwallo na matakin jiha a tsakanin ɗaliban sakandire inda Ƙaramar hukumar Anka ta lallasa Ƙaramar hukumar Tsafe da ci shida da biyar.

Wasan ya gudana ne a filin wasa na makarantar fasaha da kimiyya dake Gusau ranar Asabar .

Ƙaramar hukumar Tsafe ta fara cin kwallo ɗaya kafin zuwa hutun rabin lokaci, yayin da Ƙaramar hukumar Anka ta ci ƙwallo ɗaya bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, yanayin da yasa aka gudanar da bugun daga kai sai gola inda Ƙaramar hukumar Anka tayi nasarar cin kwallo biyar ita Kuma ƙaramar hukumar Tsafe ta ci ƙwallo huɗu.

Hakan ya bai wa ƙaramar hukumar Anka damar wakiltan Jihar Zamfara a wasan Ƙasa baki ɗaya da zai gudana a Abuja nan ba da jimawa ba.

Taken wasan na bana shine, samar da ilimi ga Kowa ta hanyar wasanni, watau “Education for all through Sports” .

Da yake jawabi a ƙarshen wasan, kwamishinan ilimi, kimiyya da ƙere-ƙere na Jihar Zamfara, Alh. Wadatau Madawaki ya jinjinawa dukkanin yan wasan tareda tabbatar da cewar gwamnatin jihar za tayi iya ƙoƙarin ta don ganin waɗanda za su wakilceta a matakin Jihar sun samu nasara a wasan Ƙasa baki ɗaya da zai gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Shima a nashi jawabin, shugaban hukumar samar da ilimi bai ɗaya reshen Jihar Zamfara, Farfesa Nasiru Anka, ya jaddada cewar hukumar sa za ta yi bakin ƙoƙarin ta don ganin waɗanda za su wakilci jihar a matakin Ƙasa sun baiwa mara ɗa kunya a wasan da za ayi matakin Ƙasa nan gaba.

Farfesa Nasiru Anka yayi kira ga sauran ɗaliban sakandire da su ka fafata a wasan ƙwallon da sauran wasanni da su Ƙara ƙaimi wajen ƙwarewa a fannin wasanni don cigaban Jihar.

By ukarofi