NELFUND ta bai wa ɗaliban Nijeriya lamunin Naira biliyan 11

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Asusun bayar da lamunin ilimi na ƙasa, NELFUND ya ce, zuwa yanzu ya raba rancen kimanin Naira biliyan 11 ga ɗalibai domin tallafa wa ilimi a ƙasar.

Shugaban hukumar, Akintunde Sawyerr ne ya faɗi hakan a yayin wata hira da Gidan Talabijin na Arise inda ya bayyana ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin an samu sauƙi a harkar Ilmi.

Sawyerr ya ce ba za a buƙaci waɗanda suka ci gajiyar lamunin su biya bashin ba, har sai bayan sun kammala bautar ƙasa da shekaru biyu ko kuma sun samu aikin yi.

Sannan, tsarin biyan lamunin zai biyo ta hanyar zare wani kaso ne da bai taka kara ya karya ba daga albashin mai ɗauke da bashin a kowane wata cikin ƙayyadadden lokaci.

Sawyerr ya ƙara da cewa, an ɗauki matakin ne da nufin sassauta jin nauyi akan masu ɗauke da bashin da ba su riga sun samu aikin da zai biya musu bashin ba.

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ƙirƙiro shirin bayar da lamunin Ilmi ga ɗaliban da suka cancanta, wanda zai ba su damar neman ilimi mafi girma ba tare da sun shiga matsalar neman kuɗi ba.

Baya ga ɗaliban Ilmi, NELFUND ta sake jaddada aniyarta ta tallafa wa fannin ilimin ƙirƙira ga matasan Nijeriya da kuma samar masu da ayyukan yi.

By Babaji