DSS ta tsige Adegboyega a matsayin babban jami’in tsaron Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Ƙasa (SSS), Tosin Ajayi, ya tsige Adegboyega Fasasi daga muƙamin babban jami’in tsaro (CSO) ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wata majiya ta ce an cire Fasasi ne daga muƙamin inda aka maye gurbinsa da Rasheed Atanda Lawal, wanda mataimakin darakta ne da ke ɗaukar horo a Cibiyar Nazarin Harkar Tsaro ta Ƙasa.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, an cire Fasasi ne daga matsayinsa da amincewar Shugaba Tinubu sakamakon wata buƙata da aka nema ta tura shi ɗaukar horo a ƙarƙashin tsangayar koyon salon iya aiki.

Rahotonni sun bayyana cewa, ana zargin sauke Fasasi da aka yi daga muƙamin nasa bai rasa nasaba da yin amfani da matsayinsa wajen yin ababen da ba su dace ba da kuma yin kane-kane ga harkoki da dama da ke da alaƙa da shugaban ƙasa.

By Babaji