Hedikwatar Tsaron ƙasa ta sanar da sabon muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa yayin da wanda yake kan muƙamin, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya tafi hutun aiki.
Kada a manta cewa an yi wasu rahotanni dangane da rashin ganin Lagbaja, inda wasu majiyoyi suka yi hasashen yana fama da matsalar lafiya.
Haka nan, an ce wannan lamari ya haifar cece-kuce daga ‘yan siyasa da wasu manyan hafsoshin sojojin da suke neman ɗarewa kujerarsa.
An haifi Lagbaja a ranar 28 ga Fabrairu, 1968, a Ilobu, Jihar Osun, inda aka naɗa shi a watan Yuni 2023, a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa na 27.
Sai dai, hedikwatar tsaron ƙasa ta bakin Manjo Janar Onyema Nwachukwu, daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Sojojin Ƙasa, ta bayyana a ranar Asabar cewa babu wani rashin shugabanci a Sojan Najeriya.
Nwachukwu ya bayyana cewa Lagbaja yana hutun aiki ne, kuma an tsara dukkan matakan da suka dace don Babban Hafsan Tsare-Tsare da Shiri na Sojoji, Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim, ya riƙe matsayin Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS) yayin da yake hutu.
Ya ce, “Ana zarge-zargen cewa akwai rashin shugabanci, inda hafsoshi ke cikin ruɗani kan abin da za su yi. Babu gaskiya a wannan zargin.
“Domin cire shakku, Rundunar Sojojin Ƙasa (NA) runduna ce mai tsari da ƙa’idoji waɗanda aka tsara sosai don kula da kowane irin yanayi. Kafin tafiya hutun aiki, an tanadi dukkan matakai da suka dace don Babban Hafsan Tsare-Tsare (Army), Manjo Janar Abdulsalami Bagudu Ibrahim, ya wakilci Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS) yayin da yake hutun aiki.
Ya ce, “Haƙiƙa, bisa tsare-tsaren da aka fitar na shekarar 2024, Rundunar Sojojin Ƙasa kwanan nan ta gudanar da jarrabawar ƙarin girma daga Kyaftin zuwa Major a Akure. Wanda yanzu haka muƙaddashi, Janar Abdulsalam ya sanya wa hannu kuma an fitar.
