NFVCB ta nuna damuwa kan yadda ake shirya fina-finai marasa inganci

*Daga yanzu dole kowane ɗan indostiri ya zama cikakken mamba mai rijista – NFVCB

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa (NFVCB), ta nuna damuwarta kan yadda masana’antar fina-finai ke samar da fina-finai marasa inganci saboda rashin aiki da ƙwarewa.

Hukumar ta nuna damuwar tata ce cikin sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Thomas Adedayo, wadda aka aike wa ɗaukacin masu ruwa da tsakin masana’antar fina-finai.

Domin kawar da wannan matsalar, Adedayo ya ce wajibi ne a dawo a riƙa aiki da ƙwarewa a harkar fim, kama daga masu rubuta labaran fim zuwa masu kwalliya da kula da fitila da sauransu.

Ya ce, hukumar za ta yi wannan aiki ne ta la’akari da ikon da doka ta ba ta kamar yadda yake ƙunshe a Sashe 2 (e) na Dokar NFVCB ta 2004, da kuma Sashe na 17 da karamin sashe na 2 da na 3 na dokokin NFVCB na 2008, wajen tabbatar da ana aiki da ƙwarewa da kuma samar da fina-finai masu inganci.

Ya ƙara da cewa, hukumar ta tsayar da ranar 22 ga Mayu don yin aikin tabbatar da ana aiwatar da dokokinta yadda ya kamata.

Don haka ya ja hankalin daraktoci da furodusoshi da sauran masu ruwa da tsaki a masna’antar shirya fina-finai da su tabbatar an bi dokokin hukumar sau da ƙafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *