Ni ce mace ‘yar Arewa ta farko da ta fara karatun aikin noma – Esther Usman

“Na yi aiki a ƙasashe ashirin da huɗu na duniya

DAGA ABBA MUHAMMAD

Honarabul Esther Usman Walabai, tsohuwar ma’aikaciyar bankin duniya (Worid Bank), ƙwararriyar masaniya a kan harkokin noma, haka kuma ƙwararriya ce a ɓangaren sanin jinsi. Esther Usman Walabai, ‘yar Jihar Adamawa ce, wadda a yanzu tana ɗaya daga cikin fitattu kuma gogaggun ‘yan siyasar jihar a Jam’iyyar PDP. Walabai ta nema takarar zama sanata a shekarar 2007, bayan ta aje aikin ‘World Bank’, ta kuma yi takarar zama ‘yar majalisar tarayya, sannan ta sake takarar zama sanatar Adamawa ta Arewa a wannan karo, sai dai duk babu wanda ta samun gurbin zama ‘yar takarar. A halin yanzu ta kafa wata ƙungiya mai suna ‘PDP Arewa Youth Support Group’, wanda za su bi dukkan jihohin Arewa 19 domin wayar da kan mata da matasa a game da zaɓe mai zuwa. A hirarta da Manhaja, Honarabule Esther Usman Walabai, ta bada taƙaitaccen tarihinta, gwagwarmayarta game da ayyukan da ta yi, dalilin kafa ƙungiyar ‘PDP Arewa Youth Support Group’ mai ya sa ta ke taimakon matasa a matayin ta na dattijuwa, a ƙasashe nawa ta yi aiki da sauran su. Ga yadda hirar ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Ki faɗa mana cikakken sunanki da tarihinki?

ESTHER WALABAI: Sunana Esther Usman Walabai, ni ‘yar Adamawa ce, amma na samu kai na a Jihar Nasarawa.

Ni dai tarihin rayuwata, da na gama makaranta na shiga aikin gona. A wancan zamanin mata ba su yin aikin gona, wato ‘Agriculture’, sai dai su yi ‘Home Economics’, inda ake girke-girke da sarrafa kayan abinci. To ni kaɗai a Arewa a lokacin 1972 na ce sai dai abin da maza su ke yi zan, sai dai in tuƙa ‘Tractor’, da haka ne na shiga ‘Agriculture’.

Daga nan OND, HND, na yi digiri na na farko, na yi ‘masters degree’ a cikin dukka Agriculture’, kuma dukka yawanci tare da maza ne. Amma duk da haka bai hana ni yin wasu ayyuka ba, musamman ma a faɗakar da mutane a kan ayyukan mata da amfanin mata a sha’anin rayuwa ko raya karkara ko kuma raya iyali, in mata ba su ciki ko da menene ake yi, ba za a ce maza ne kawai za su zama su tada iyalinsu ba, bare ma a ce mutane a karkara.

Daga can na fara aikin ‘gender’, wanda ake ce wa ‘gender issues’, wanda duk abin da ya samu mata za a zauna a magance, don su mata su samu su shiga fannin ayyuka a duniya. Na yi aiki a qasashe ashirin da huɗu na duniya.

Na yi aiki a ‘Worid Bank’, na yi aiki lokacin ‘North East’ a Barno, na yi aiki a Legas da sauran ƙasashen ‘West Afrika’, irin su Ghana, Burkina Faso, Mali da dukka waɗannan duk na je. Mun tafi har Israel musamman don ganin yadda ake sarrafa lambu, tunda su su na da ƙarancin ruwa, yadda za a yi amfani da roba a jefa shi ƙasa ya ɗaukar ruwa a sa a kowanne gindin yabanya ko kuma shuka.

Menene matsayinki a tafiyar Atiku Abubakar?

Tafiyar Atiku dai ba yau na fara ba. Tun 2007 lokacin da na bar ‘World Bank’, a 2006 a ƙarshen shekara, ba kuma na bari don komai ba ne, da kai na, da sona na bari, ba wai dakatar da ni aka yi ba. Haka kuma duk inda na tava aiki kaɗan, za ka ga na aje, ko na siyasar ma a kwanaki 2019 aka ba ni ‘Special Adviser’ a Adamawa ni da kai na na ce ba na so ba zan yi ba.

To ko mai ya sa haka?

Ra’ayina ne, ra’ayin da bai je da nawa ba, sai na ce ba na so.

Ba ki tunanin yawaitar ire-iren ku zai ba wa mata ƙwarin gwiwar fito wa su jefa ƙuri’a?

Wannan na sha faɗa, ko ina in zan yi magana, sai na yi maganar mata da matasa, ba za a tava kafa gwamnati a ƙasar nan in ba mata da matasa. Mata ma suka fi yawa, a wurin iyali za ka je ka tarar mata shida ko bakwai, shi kaɗai ne maigida da yara ƙanana. Shi ya sa duk inda aka ga na yi aiki, sai na kawo a yi mata a ciki, ta yadda za a zauna a inganta su, a ƙara masu ƙarfi, a ƙara masu ilimi, sannan kuma kowanne irin aiki suke yi, in dai sun samu ƙwarewa a ciki ba za su samu damuwa ba.

Menene manufar ƙungiyar ‘PDP Arewa Yourt Support Group’ da ki ka kafa?

‘PDP Arewa Yourt Support Group’ dai ƙungiya ce na tarayya, in na ce tarayya ba Ina nufin na haɗa ba ne da jihohin Kudu ba, amma jihohi sha tara a Arewa, ya kamata ce su ma matasa su na da baki da kuma ‘yanci, su samu yadda za su yi su taimaka wa ‘yan siyasa ko kuma abubuwan da zai taimaki ƙasar ko garinsu.

Jama’a za su yi miki kallon shekarunki sun ja, amma kuma ki na taimakon matasa ko me ya sa haka?

Na gode da wannan tambayar. Babu yadda za a ce matasa za su tashi haka ba tare da shawarar babba ba. Ni uwa ce, ni kaka ce ma zan ce, amma na ga cewa, su matasan su na da amfani ne, na tashi Ina yi masu kokuwa, Ina yi masu faɗa domin su samu su mori tafiyar da ake yi. To ai ba laifi ba ne, dole kowanne irin fanni da ake yi sai da babba.

Amma ki na samun goyon bayan matasan?

Ƙwarai da gaske, Ina samun goyon bayan su sosai. Su na mamakin yadda ba na cewa a je a samu tsofaffi, tsofaffi mun riga mun sha zamani, mun ci zamaninmu, ya kamata mu raya bayan ‘ya’yanmu ko kuma matasanmu in mu na so su gaje mu.

To in ba haka mu ka yi ba, yaushe ne za su fara? Amma kuma ban ce in kai matashi ne ka je ka naɗe hannunka, ka yi tsammani wai za a kawo ma ka, dole sai ka yi ƙoƙari, ka yi nazari, ka je ka yi iya ƙoƙarin yadda za ka yi ka samu, na farko ka na da ilimi, na biyu ka na ƙwarewar, na uku ka na da sanin jama’a, ba wai kawai gidanku ko unguwarku kawai ba, na huɗu ka na da gaskiya a cikin duk abin da ka ke yi, ba wai a ce abin na wasa ba ne, yadda in an ɗan ba ka muƙami ka zama kai ne oga gabaɗaya ba. Dole duk abin da za ka yi ka tabbatar cewa haƙƙin mutanen da ka ke wakiltar su yana kanka don haka dole ka daure ka yi gaskiya. Wannan shi ne dalili.

A baya kin fito takarar sanata a Adamawa ta Arewa, daga baya kuma aka ji ki shiru. Menene dalili?

Na gode. Da na bar Bankin Duniya ‘World Bank’, na zo saboda in yi takarar sanata, kuma kamar yadda na faɗa ma ku na bari ne da son ra’ayina, ba an kore ni ba ne ko kuma lokacina ya yi, sai na ce na tabbata in na zo akwai abin da zan taimaka kuma in bada gunduma na da jihata da ayyukan da suka kamata da zai inganta rayuwar karkara da sauran su.

Da na zo da farko a 2007, ga Habibu Musa, su ne su ka yi ta yin talla ta babu inda ba mu shiga ba a Jihar Adamawa, mu ka gama komai, kuma babu wanda ya yi irin wahalar da mu ka sha, babu wanda ya fito, sai ranar ƙarshe ba zan manta ba, ranar Laraba, ranar Asabar za a yi ‘primaries’, shi ne aka kawo wani ana cika masa fom, daga wurin na san cewa akwai wani abu. Wato ni abin da na gane da siyasa, shi ne in ba ka na da wani a sama ba, ka na da ubangida ba, in ka zo, duk yadda ka kai da iliminka, duk yadda ka kai da ƙwarewarka ba za a ɗauke ka ba.

Ballantana ka zo wuraren da ba ka sani ba, suna ganin kai wannan fa ba za ta bi na mu ba, ba za ta karɓi shawararmu ba, Ina tsammanin shi ya sa da na yi wancan ɗin aka ƙwace, a cikin kwana uku aka karɓe, ko ina aka je ana sai Walabai, sai a rinƙa cewa ai ta janye, yanzu wane ne, ba na so in kira sunan mutumin.

A nan dai ki na so ki nuna wa masoyanki ba ke ki ka janye da kanki ba, jam’iyya ce ta nemi haka?

Ƙwarai, haka ne. Abin da ya sa zan ce jam’iyya ce ta yi haka, mai ya sa shi ba za a ce masa ya haƙura ba, sannan kuma jam’iyya ce ta ɗauke da ‘nomination form’ ana za na masa. In dai jam’iyya ba ta yi ba, ai ba za a yi wannan ba, da bakin jam’iyya a ciki, zan iya faɗa da jam’iyya ne.

A kan wannan wani mataki ku mabiya jam’iyya ku ka ɗauka?

Ba na tsammani an ɗauki wani mataki, amma fa an yi fushi. Domin duk da ka je za ka ji ana cewa idan ba wannan matar ba, babu wanda zai yi mana aikin da ya kamata. Amma dai tunda su ka yi zaginsu, ni ba na faɗa da babba, faɗan da ya fi ƙarfinka aka ce ka maida shi wasa.

To na biyun sa, da na ga wancan bai yiwu ba, na siye form na reps, ranar da na siya zan saka a cikin file, wani ubangidana ya zo, ya ce shi ma zai tsaya, na ce ni zan tsaya da kai? Haka na haƙura. Na sake yin na uku, shi ne ‘last one’ na ‘senate’, zan declairation, Ina da takardu, Ina da shaidu, sai babban maigidanmu ya kira ni ba na so in faɗi sunansa, wai ya kamata in haqura tunda ba ni da lafiya bai kamata in nemi takara ba, na ce haka ne, to ya zan yi yanzu, kuɗin da na kasha fa, ya ce kar ki damu. To har yau, har gobe ban sake ganin su ba.

Esther Walabai

A yanayi na rashin tabbas, a kan taɓarɓarewar tsaro, ta wacce hanya za ku bi domin isar da tallar ɗan takararku da kuma jam’iyyarku?

Tsaro na da muhimmanci ƙwarai da gaske, domin duk ƙasa ko kuma jihar da bata da tsaro, mutane ba za su yi walwala ba, kuma ba za su yi abin da ya kamata ba, don ana tsoro. Don haka, dole a wayar da kan mutane, birni da karkara, kamar yadda na ke faɗa ma ku kullum, in zan yi magana zan ce, in akwai wayar da kai ko inganta rayuwar mutane, duk wannan sai an fara daga can ƙasa, mutanen da suke can garuruwa ko ƙauyukan da ke yi, sun riga sun san menene zafin da su ke ji, dole in sun san yadda za su kare kansu, su kare jiharsu, musamman matasa, su ne ya kamata su san yadda za su kula da garuruwa da yankin da suke zama. Saboda in an ba su ilimi na tsaro, dole su tsare jihohinsu da mazaunansu.

Wane jan-hankali za ki yi ga matasa da kuma dukkan ‘yan takarar jam’iyyarku?

‘Yan takara a Jam’iyyar PDP na gode wa Allah, na tabbata mun zaɓi masu adalci. Mu na so kuma su riqe al’ummarsu sosai, saboda in ba sun riƙe al’ummarsu da kyau ba, kuma an yi gaskiya da su, kuma ko wani irin taimakawa ne da zai sa ya inganta rayuwar mutane, dole ne kuma su samu su goyi bayan su, amma in an zauna an yi sake, an zubar da waɗanda ya kamata a taimaka masu, ba zai yiwu ba.

Don haka matasa da mata Ina so ku riƙe al’ummarku haka a hannu. Domin in ba ku ne ku ke bada shawarar ba, wani ko wata ba zai je Abuja ya samu shugaban ƙasa ko kuma party chairman ba. Dole sai mun fara, ‘charity begins at home’, sai mun zauna mun gyara al’ummarmu, mun tabbatar da cewa masu gaskiya ne suke rulling, kuma waɗanda suka cancanta, to a haka za mu yi gaba.

Na gode.

Nima na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *