Ni ne babban ƙalubalen NNPP da Kwankwaso, ba APC da Shugaba Tinubu ba – Doguwa ga Jibrin

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan albarkatun man fetur, Hon. Alhasan Ado Doguwa, OON, ya mayar da martani game da kalaman Abdulmumini Jibrin da ke wakiltar mazaɓar Ƙiru/Bebeji na cewa shi barazana ce ga jam’iyyar APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar Kano.

Cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, Doguwa ya nanata batun ƙalubalantar Jibrin a yayin mayar masa da martani kan cewa ya yi magana kan zargin da ya yi masa (Jibrin) a makon da ya gabata na kashe mutum 7 da kuma jagorantar wata tawagar ƴan daba wajen kai hari ga tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, don haka Jibrin ya ce Doguwa barazana ne ga APC da Shugaba Tinubu a Kano.

A yayin bada amsa game da kalaman Jibrin ne, Doguwa ya ce “kamar ɓarawo ne da dare” Jibrin ya guje wa magantuwa kan zargin kisan, ya na mai cewa ƴan sanda sun kama Jibrin tare da wasu mutum 70 da ake zargin su da hannu cikin aikata laifin.

Ya ce, “Ni ba ɗan siyasar da ya dogara da wani ba ne a Kano, madadin haka kamar yadda ku ka sani, Ni kadara ce, kuma abin alfahari, sannan jigo a APC a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.”

“A yau ina mai bugun ƙirji a siyasar Kano cewa Ni kaɗai ne halstacce kuma zaɓaɓɓen ɗan takarar APC a baki ɗaya Kano ta Kudu. Duk da sauye-sauye, na dawo kan kujerata ta Majalisar Wakilai da maki na ƙololuwa,” inji Doguwa.

Ya kuma ce, shi ne babban barazana ga sabon shigar gwamnatin NNPP da mai iƙirarin shi ɗaya ne daga cikin manyan ƙasa, Rabi’u Kwankwaso wanda ya ce takwaransa ne a harkar siyasa tun a jamhuriyar ta uku.

Haka kuma, Doguwa ya yi tsokaci kan gazawar gwamnatin a jihar, ya na mai cewa jam’iyyar (NNPP) madadin ta mayar da hankali wajen bunƙasa tattali da zamantakewar al’ummar jihar, abin takaici ta koma ayyukan cin dunduniya da siyasar cin mutunci da ɗaukar mataki.

Har’ilayau, Doguwa ya nemi shugabancin APC ya naɗa shi a matsayin shugaba kuma Darakta-Janar na yawon neman zaɓenta a Kano, ya na mai cewa da yardar Allah zai kawo Kano kafin rana ta yi a ranar zaɓe a shekarar 2027.

Kazalika, ya ce a shekaru 33 da ya shafe a Majalisar wakilai, ba a taɓa dakatar da shi ko samun sa da wani laifi ba kasancewar ya na ƙoƙarin kiyaye aikinsa da gaskiya tare da girmamawa har ga abokanan aikinsa da waɗanda ke sama da shi.

Daga ƙarshe, ya ce za a samu tabbacin halinsa na mai son zaman lafiya da ɗabi’unsa daga mutanen mazaɓarsa, sarakunan gargajiya da malamai. Sannan, da gudunmawarsa ga hukumomin tsaro irinsu ƴan sanda, sojoji, ƴan ‘Civil Defence’ da kuma ƴan banga da ya ke taimaka mu su ta hanyoyi da dama.

By Babaji