.. An kashe mutane 565 a shekarar 2024
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Nijeriya ta kasance a matsayi na shida a ƙididdigar ta’addanci ta duniya a shekarar 2025 da maki 7.658, inda ta tashi daga matsayi na takwas a 2023 da 2024.
Dangane da rahoton shekarar 2025 da aka fitar a ranar 5 ga Maris, 2025, Burkina Faso ce ke kan gaba da maki 8.581, Pakistan (8.374), Syria (8.006), Mali (7.907), da Nijar (7.776), wacce ta zo ta biyu zuwa ta biyar, bi da bi.
Somalia (7.614), Isra’ila (7.463), Afghanistan (7.262), Kamaru (6.944), Myanmar (6.929), Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (6.768), Iraƙi (6.582), Indiya (6.410), Colombia (6.381), da Rasha (6.267) a matsayi na bakwai zuwa goma sha shida.
Rahoton ya kawo rahoton mutuwar mutane 565 masu alaƙa da ta’addanci a Nijeriya a shekarar 2024, wanda ya nuna ƙaruwar mace-mace a cikin shekaru biyu da suka gabata.
“A duniya baki ɗaya, mace-macen ta’addanci ya ragu da kusan kashi uku tun bayan da aka samu raguwar adadin a shekarar 2015, inda Iraƙi da Nijeriya suka samu raguwa mafi girma. Adadin waɗanda suka mutu a Nijeriya ya kai 2,101 a shekarar 2014, kafin ya ragu zuwa 392 a shekarar 2022, matakin da ya kasance mafi ƙaranci tun 2011. Sai dai, adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru da kashi 34 cikin 100 a shekarar 2023 zuwa 533, sannan ya kai 565 a shekarar 2024.”
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa ƙungiyar IS-Sahel da ke da ƙarfi a yankin Liptako-Gourma—yankin da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali da Nijar — ta faɗaɗa ayyukanta zuwa ƙasashen Aljeriya da Benin da kuma Nijeriya. A shekarar 2024, ƙungiyar ta kai hare-hare 16 a Nijeriya, 12 a Nijar, 6 a Mali, ɗaya a Burkina Faso.
Bugu da ƙari, adadin ƙasashen da aƙalla harin ta’addanci ɗaya ya shafa ya ƙaru daga 58 zuwa 66, adadi mafi yawa tun shekarar 2018.
“Ta’addanci ya ci gaba da zama barazana ga duniya baki ɗaya, tare da shekarar 2024 da ke nuna wata shekara ta sauya salo da kuma fuskantar ƙalubale. ƙasashe da yawa sun fuskanci taɓarɓarewar tsaro, inda 45 suka ba da rahoton ƙaruwar tasirin ta’addanci, yayin da 34 kawai suka samu ci gaba – karo na farko cikin shekaru bakwai da ƙasashe da yawa suka ƙara taɓarɓarewa fiye da ingantawa.”
Yankin Sahel ya zama cibiyar ta’addanci a duniya, wanda ya kai kashi 51 cikin 100 na yawan mace-macen ta’addanci a shekarar 2024, wanda ya ƙaru kusan sau goma tun daga shekarar 2019. A dunƙule, yawan mace-macen da ke da nasaba da tashe-tashen hankula a yankin ya zarce 25,000 a karon farko tun bayan da aka kafa wannan ƙididdiga, inda aka alaƙanta ta’addanci 3,885.
“Biyar daga cikin ƙasashe goma da ta’addanci ya fi shafa suna yankin Sahel. Duk da cewa Burkina Faso ita ce ƙasar da ta fi fama da matsalar, duk mace-mace da hare-hare sun ragu a shekarar 2024—ya faɗi da kashi 21 cikin ɗari da kashi 57, bi da bi. Koyaya, ƙasar har yanzu tana da kashi ɗaya cikin biyar na yawan mutuwar ta’addanci a duniya.”
Rahoton ya kuma bayyana raunin da ake samu wajen yaƙi da ta’addanci, inda ya buga misali da Nijar.
“Nijar ta samu ƙaruwar mace-mace masu alaƙa da ta’addanci a duniya a shekarar 2024, wanda ya ƙaru da kashi 94 cikin ɗari zuwa 930. Wannan ya sauya ci gaban da aka samu a shekarar 2022 lokacin da ƙasar ta samu ci gaba mafi girma na biyu a tasirin ta’addanci. Al’amarin Nijar ya nuna cewa nasarorin da aka samu a Burkina Faso na iya zama na wucin gadi.”
