Nijeriya na buƙatar ‘yan sandan jihohi – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamnati da ta ƙirƙiro da ‘yan sandan jiha a Nijeriya.

Obasanjo ya ce Nijeriya na buƙatar ‘yan sandan jiha domin magance ƙalubalen tsaron da ke addabar ƙasar.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa mai taken “Haƙƙin da ke kan al’umma wajen gina ƙasa’, a wajen murnar cikar Kulub ɗin Island da ke Legas shekara 78 a ranar Juma’a.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce wuraren da ba su fama da tashe-tashen hankula ne kawai ke da tabbaci da yaqinin samun ci gaba ɓangaren gina ƙasa.

A cewar sa, “Kamar yadda na faɗa a baya, yanzu ma zan sake faɗa. Ya kamata Nijeriya ta ƙirƙiro da ‘yan sandan jiha a dukkan jihohin da muke da su, wadatattu, domin su magance matsalar tsaron da ya yi wa ƙasar katutu.

“Samar da muhallin kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne abu na farko da ya wajaba a kan gwamnati.

“Babu wata ƙasa da za a ce ta ginu a cikin yanayin rashin zaman lafiya, tsaro da kuma kwanciyar hankali, saboda haka haƙƙi ne da ke wuyan Shugaban Ƙasa ya yi duk mai yiwuwa don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.”