Nijeriya ta fi dukkan Afirka shigo da janareto – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani sakamakon bincike da Hukumar Sabunta Makamashi Ta Duniya  (IRENA) ta gudanar ya bayyana cewa, Nijeriya ita ce jagaba wajen shigo da injin janareto a faɗin ƙasashen Afirka gabaɗaya. 

Rahoton mai taken ECN ya bayyana dalilan da suka sanya ‘yan Nijeriya suka dogara matuƙar dogara da janareto da kuma illarsa ga tattalin arzikin ƙasar da sana’o’i. 

Sana’o’i da gidaje da dama a ƙasar sun dogara ne kacokan a kan injinan janareto don samun wuta saboda ƙarancin wutar lantarki a ƙasar. 

Saboda haka, rashin isasshen sinadarin gas, tangarɗar na’urori da rashin wadatar tashoshin wutar su na daga cikin dalilan da suka zama ummulaba’isin na rashin samun hasken lantarki.

Matsananciyar wahalar wutar ta sanya Nijeriya ta yi zarra wajen shigo da mafi yawan janareto a Afirka. Wato daga cikin janareta miliyan shida da rabi da ake shigo da su izuwa Afirka, Nijeriya ce ta ke da miliyan uku. 

Haka zalika, tsadar cajin wutar lantarki ma yana daga cikin dalilan da suka sa wasu wuraren a Nijeriya suka dogara da janareton don su rage kashe kuɗin biyan kamfanonin rarraba wutar lantarki. 

A wani rahoto kuma da ‘Stears Business’ suka yi, gidaje da wuraren sana’o’i a Nijeriya sukan kashe ƙiyasin Dalar Amurka Biliyan 14 wajen sayen man jananreto a kowacce shekara.

Haka zalika, wasu sahihan rahotannin ma kuma sun bayyana cewa, Nijeriya ta kashe Dalar Amurka biliyan  $5.26 wajen shigo da injin janareto da sauran injinan lantarki da kayan aiki a tsakanin shekarar  2020 da 2021 kawai.

Wannan ya sa sana’o’i sun yi tsada a Nijeriya, kayan da ake sanarwar a Nijeriya kuma sun fi na waje tsada matuqa da kusan ninki uku saboda tsadar lantarki. 

A kan haka sakamakon bincken na IRENA ya bayyana cewa, Nijeriya ta na buqatar zuba kuɗaɗe sosai don kusan aƙalla Dalar Amurka 34.5 a sashen wutar lantarki matuƙar ana son a samu wadatacciya kuma ingantacciyar wutar lantarki.