Bankuna za su fara aiki ranar Asabar don canza tsofaffin kuɗaɗen masu ajiya – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya, CBN ya bayyana cewa, bankuna za su dinga aiki a ranakun Asabar don samun damar canza wa masu ajiyarsu tsofaffin kuɗaɗensu zuwa sababbi.

Kama Ukpai, shugaban tawagar CBN ta jihar Ebonyi a kan sababbin takardun Naira, shi ya bayyana hakan ranar Juma’ar da ta gabata a yayin gangamin wayar da kai ga ‘yan kasuwa a kasuwar Eke dake Afikpo.

Mista Ukpai ya shawarci al’umma da su ziyarci bankuna su ajiye tsofaffin kuɗaɗensu a canza musu da sababbi. Domin kuwa a cewar sa, babu gudu ba ja da baya wajen tabbatar da daina amsar tsofaffin takardun kuɗin daga ranar 31 ga watan Janairu, 2023.

“Bankuna za su dinga aiki ranar Asabar saboda wannan dalili. A yanzu haka tawagar CBN tana nan a Ebonyi don tabbatar da an bi wannan dokar. Kuma ba mu ba wa kowanne banki umarnin daina karvar tsofaffin kuɗin ba”. Inji shi.

Ya ƙara da cewa, tawagarsa ta kai ziyara zuwa bankuna 14 a garin na Abakaliki, kuma sun samu bankuna 13 daga cikin 14 suna ba wa mutane tsofaffin takardun kuɗaɗen ta injin cirar kuɗi (ATM).

Kuma a cewar sa, sun yi magana da waɗancan bankuna da suke fitar da tsofaffin kuɗaɗen, kuma ya bayyana wa al’ummar gari cewa, sababbin takardun kuɗin nan fa suna nan a wadace.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani banki da ya cigaba da ba da tsofaffin kuɗi a injin ATM ɗinsa domin a gurfanar da shi.

Sai dai shi kuma Johnson Inya-Oka, Chairman, shugaban haɗakar ‘yan kasuwa na kasuwar Afikpo, bayan godiya ga CBN a kan wannan wayar da kan al’umma, ya yi kira ga mahukuntan da abin ya shafa a kan a ƙara wa’adin daina aiki da tsofaffin kuɗin.

Domin a cewar sa har yanzu ma wasu ‘yan kasuwar ma ba su tava yin ido huɗu da sababbin takardun kuɗin ba, a don haka ana buƙatar ƙarin lokaci na mutane su gane sabon kuɗin, da yadda za su iya rarrabe shi da shi da tsohon kuɗin. Da kuma yadda za su yi amfani da na’urori da fasahar zamani na hada-hadar kuɗi.