Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar da ke bayar da lamuni kan harkar noma ta Babban Bankin Nijeriya (NIRSAL) ta bayyana samun gagarumar nasara a ayyukanta na bana, inda ta taimaka wajen samun fiye da Naira Biliyan 70 a matsayin tallafin kuɗi daga bankuna don bunƙasa harkokin noma da kasuwancin noma zuwa ƙarshen shekarar 2025 — abin da ke zama shekara mafi nasara tun bayan kafuwarta.
Tun daga lokacin da aka kafa ta a 2013, wannan sakamako na bana ya kai kusan kashi 25 cikin ɗari na jimillar Naira Biliyan 270 da hukumar ta taimaka wajen samarwa ga ɓangaren noma tun farko. Wannan kuwa na nuna tasirin sabon tsarin aiki da hukumar ta kafa ƙarƙashin sabon kwamitin gudanarwa da shugabancin zartarwa.
A cewar bayanan hukumar, wannan sauyi ya zo ne a lokaci mai muhimmanci, yayin da rancen bankuna ga manoma ke ta raguwa – daga kashi 6.18% na jimillar rance a 2022 zuwa 4.82% a 2024. Haka kuma, ci gaban ɓangaren noma ya ragu daga kashi 2.5% zuwa 1.7% a wannan lokaci.
Sai dai ta hanyar amfani da tsarin nazarin ‘value chain modelling’, bayar da tallafin fasaha ga manoma da cibiyoyin kuɗi, tare da amfani da tsarin raba haɗarin bashi (risk-sharing frameworks), NIRSAL ta samu nasarar dawo da aminci daga bankuna, wanda ya sa aka fara zuba sabbin kuɗaɗe a muhimman sassa kamar hatsi, coco, man kaɗe da kiwo.
Rahoton ya nuna cewa wannan cigaba ya haifar da ƙarin samar da kayayyakin noma a cikin gida da kuma ingantacciyar ma’amalar ciniki ta ƙasashen waje, inda sama da kashi 32 cikin ɗari na kuɗin da aka taimaka da su suka tafi wajen fitar da kayayyakin noma da aka ƙara musu daraja zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma, kaso na noma cikin rancen bankuna ya ƙaru zuwa kashi 5.33% a watan Mayun 2025, abin da ke nuna dawowar sha’awar masu ruwa da tsaki a harkar. Haka ma, sabbin bankuna biyu da aka ba lasisi sun shiga ɓangaren noma bisa tsarin NIRSAL, suna cikin waɗanda suka bada gudunmawar Naira biliyan 70 da aka samu har yanzu a bana.
Da yake tsokaci kan wannan nasara, Shugaban NIRSAL, Sa’ad Hamidu, ya ce, “Ko da yake Naira biliyan 70 ba ta kai yawan buƙatun kuɗin noma a Nijeriya ba, muhimmancin ta yana da girma. Ta tabbatar cewa noma na iya samun kuɗi ta hanyar kasuwanci mai dorewa. Idan aka haɗa jari da tallafin fasaha da tsarin kariya daga haɗari, noma zai zama fanni mai ƙarfi, ɗorewa, kuma mai gogayya da duniya.”
Hamidu ya ƙara da cewa hukumar tana da tabbacin cimma burinta na Naira biliyan 150 kafin ƙarshen 2025.
“Ba mu kai lokacin girbi ba tukuna — lokacin da ‘yan kasuwa ke neman rance don siye da adana hatsi, ko lokacin da manyan dillalan takin zamani ke fara shirin shuka. Wannan ke ba mu cikakken dalilin sa ran ƙarin nasarori,” inji shi.
Baya ga adadin kuɗaɗen da aka taimaka da su, NIRSAL na ƙoƙarin sauya tsarin bayar da rance ga manoma, ta hanyar samar da tsarin haɗin kai daga gano masu buƙata, tsarawa, ba da shawara, har zuwa bayar da tabbacin rance. Wannan ya sa kamfanonin noma da ake ganin ba su cancanci rance ba a baya, yanzu suna iya samun kuɗi cikin sahalewa.
