
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
La’akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe a watan Agusta, hukumar shige da fice, NIS ta sanar da dakatar da neman zuwa hutu ga ma’aikatanta na wucin-gadi.
Kwamturola Janar ta hukumar, Misis Kemi Nandap ta bada umarni ga shugabannin shiyyoyi da na jihohi da kuma na yankuna, inda ta ce akwai buƙatar aiki na musamman a kan iyakokin ƙasa domin tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Kenneth Udo ya fitar, hukumar ta ce tana shirye-shirye domin tsare duk wani kutse da ka iya tunkaro ƙasar daga waje da zai yamutsa al’amari.
Zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya ya biyo bayan wacce ƴan ƙasar Kenya su ka yi a makonnin da su ka gabata kan hauhawar kuɗin haraji wanda hakan ya tilasta wa shugaban ƙasar sauya matsayarsa.
An shirya zanga-zangar ne musamman ta kafofin yaɗa labarai na zamani kamar yadda ya ke faruwa a Nijeriya.
