Majalisar Wakilai ta shirya neman a tsige Kyari daga shugabancin NNPC

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Majalisar Wakilai ta yi barazanar kiran a tsige shugaban kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPC), Mele Kyari idan ya cigaba da takurawa ayyukan matatar Ɗangote.

Mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese ya faɗi hakan a yayin hira da manema labaru a Abuja.

Haka nan, Agbese ya ce Majalisar ta bayyana goyon bayanta game da tsige shugaban hukumar tace man fetur ta Ƙasa (NMDPRA), Umar Farouk, yana mai cewa NNPCL da NMDPRA sun nuna kushewarsu da ƙiyayya ga matatar Ɗangote wanda hakan ya haifar da matsaloli wa ƙasa Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, tuni dai Majalisa ta umarci shugaban ƙasa ya cire Umar Farouk inda ya ce matuƙar Kyari bai gaggauta dakatawa daga matsa wa matatar ba, to za su nemi shi ma a tsige shi kamar yadda su ka yi wa takwaransa na NMDPRA.

Bugu da ƙari, kwamitin Majalisar na musamman kan binciken satar mai da asara, yana binciken masu-ruwa-da-tsaki a ɓangaren mai, sannan ya ƙuduri aniyar yin bincikensa ba tare da tsoro ko yafiya ba.

By Babaji