
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Cibiyar tabbatar da dokoki wa al’umma, CISLAC ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta tsara jadawalin magance koken ƴan ƙasa a madadin sanya takunkumi ga zanga-zanga.
Daraktan CISLAC, Kwamared Auwal Musa Rafsanjani ya nuna buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa game da matsalolin hauhawar farashi, rashin aikin yi, rashawa, rashin tsaro da kuma rarrabewar cibiyoyi.
Rafsanjani ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin bada kariya ga masu zanga-zanga, yana mai cewa dokar ƙasa ta amince da zanga-zangar lumana.
Haka nan, ya bukaci ƙananan hukumomi da jihohi su bi hanyoyin da suka dace wajen fuskantar matsalolin bisa tsari madadin takura wa ƴan zanga-zangar wanda hakan kan iya haifar da tarzoma.
Kazalika, ya gargaɗi rundunar soji da ta guji shiga lamuran da su ke alhaki ne a kan Ƴan sanda da hukumar DSS domin kauce wa tashin-tashina.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga masu zanga-zangar da su sanya ido tare da lura da waɗanda ka iya tada rikici a lokacin zanga-zangar, yana mai neman gwamnati ta ƙyale su su bayyana ra’ayinsu game da matakan gwamnati kamar yadda dokar ƙasa ta bada dama.
