NLC ta bayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani biyo bayan gazawar gwamnati wajen cimma buƙatunta.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NLC, Benson Upah, shi ne ya bayyana shiga yajin aikin a ranar Juma’a.

Tun da fari, sai da NLC ta yi yajin aiki na kwana biyu a matsayin gargaɗi ga gwamnati, sannan daga bisani ta bai wa gwamnatin wa’adin mako biyu na gwamnati ta yi abin da ya kamace ta.

Wa’adin mako biyun ya ƙare ne a ranar Juma’ar da ta gabata, ba tare da gwamnatin ta biya buƙatun NLC ɗin ba don haka ƙungiyar ta bayyana shiga yajin aikin ka’in da na’in.

Upah ya jaddada cewa babu buƙatar ƙungiyar ko guda da gwamnatin ta cimma.