Mohbad: Dalilinmu na harba barkonon tsohuwa a Lekki – ‘Yan Sanada

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana a ranar Juma’a cewa, ta harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa taron jama’a da aka haɗa a babbar ƙofar gari a Lekki a ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce jama’a sun yi dandazo a yankin ne don nuna alhini da kuma jana’izar mawaƙin nan Ilerioluwa Oladimeji Aloba (Mohbad) a Victoria Island, Legas.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, “Babu harsashi ko guda da aka harba. ‘Yan sanda sun yi amfani da salon tattalin irin taron jama’ar da aka haɗa ba bisa doka ba.

“Ba a samu asarar rai ba, haka ma babu wanda ya ji rauni,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, ‘yan sanda na sane da labarin ƙarya da ake yaɗawa game da batun.

“Ya kamata a sani cewa, an cimma yarjejeniya tsakanin ‘yan sanda da waɗanda suka shirya taron, cewa ba za a wuce ƙarfe 8 na dare ba, sannan za a kammala taron a Muri Okunola Park, da ke Victoria Island.”

Jami’in ya ce sun amince a kan taron ba zai kai yankin babbar kofar shiga gari ta Lekki ba duba da yadda ake zirga-zirga a yankin.

Ya ce bayan kammala taron a Muri Okunola Park kamar yadda aka amince, daga bisani sai wasu mahalarta taron suka fara haɗa dandazo a babbar ƙofar gari da ke Lekki.

Wanda a cewarsa, manufarsu ita ce su assasa gwagwarmayar nema wa marigayin adalci mai taken, #justiceforMohbad.

“Ganin cewa sun bijire wa yarjejeniyar da aka cimma, hakan ya sa ‘yan sanda suka gayyato waɗanda suka shirya taron inda suka haɗa hannu wajen korar jama’a don tabbatar da lumana,” in jami’in.