Daga SANI AHMAD a Abuja
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta tara Naira biliyan 1.95 daga fasinjoji a zangon farko na shekarar 2025, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 37% idan aka kwatanta da zangon farko na 2024.
A cewar rahoton, fasinjoji 929,553 ne suka yi amfani da jirgin ƙasa a lokacin wanda hakan ke nuna, ƙaruwa da kashi 37.65% daga shekarar da ta gabata.
Haka kuma, kayan da aka ɗauka sun kai tan 181,520, yayin da aka samu Naira miliyan 657 daga jigilar su wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 8%.
Rahoton ya ƙara da cewa wasu kuɗaden shiga sun haura zuwa Naira miliyan 115.68, inda aka samu karuwa da sama da kashi 355%.
A zangon ƙarshe na 2024, NBS ta ce fasinjoji sama da miliyan ɗaya ne suka yi amfani da jirgin ƙasa, yayin da kuɗin shiga daga fasinjoji ya kai Naira biliyan 1.92.
