Dalilin da ya sa NUPENG ta kira Oshiomhole ‘butulu’ kan kalamansa game da yajin aikin PENGASSAN

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta NUPENG a ranar Litinin ta caccaki Adams Oshiomhole, Sanata mai wakiltar Arewacin Edo kan kalamansa game da yajin aikin da ta yi a baya-bayan nan, tana mai bayyana shi da “mayaudari”.

NUPENG ta bayyana hakan ne a cikin jawabin da shugabanta, Williams Akporeha da sakatare-janar ɗinta, Afolabi Olawale, suka sa wa hannu suna mai bayyana abin da sanatan ya yi da cin amanar tsarin da ya a baya ya kasance shugaban da yake ɗabbaƙa shi.

Oshiomhole, wanda ya yi suna saboda irin salon jagorancinsa a lokacin da yake shugaban ƙungiyar ‘yan ƙwadago a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

“ƙoƙarin da yake yi nuna ma’aikata sun yi ba daidai ba saboda neman haƙƙinsu ta hanyar lumana abin takaici ne da ke nuna yadda bai ɗauki ƙungiyar ƙwadago da ta duniya (ILO) da ƙima ba,” inji ƙungiyar.

ƙungiyar ma’aikatan ta ƙara da cewa matsayar da ɗan majalisar ya ɗauka ya ci karo da tuwasun da suka samar da dokokinta, inda ta zarge shi da ɗaukar ɓangaren masu kamfanoni a maimakon na ma’aikata.

Oshiomhole a ranar 3 ga watan Oktoba ya shaida wa gidan talabijin na Arise cewa yajin aikin da ƙungiyar (PENGASSAN) ta shiga kan korar ma’aikata 800 ‘yan asalin Nijeriya da matatar ɗangote ta yi an yi gaggawa kuma babu adalci ga sauran ma’aikata.

Ya ce, a yayin da ‘yancin da ƙungiyar ke da shi abu da Ubangiji ya ba ta, amma matakin da ta ɗauka na amfani da dambarwar wajen tafiya yajin aiki zai gallaza wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

“Abin da ban tabbatar ba shi ne yadda PENGASSAN ta gaggauta ta’azzara lamarin zuwa mataki na gaba wanda ya kai ga rufe ɓangaren man fetur,” inji Oshiomhole.

“Ina tunanin cewa wannan mataki ne na kare wasu ma’aikata kuma bai da ce ku jefa ayyukan wasu cikin haɗari ba.”

Sanatan ya ce ƙungiyar ya kamata ta sake duba ƙalubalen da wannan mataki nata ka iya jawowa sauran ‘yan Nijeriya.

“Ta yaya wanda ya ke ba wa gurɓatattun ‘yan siyasa shawara zai shiga APC domin a yafe masa kurakunsa yake da ƙarfin guiwar da zai yi wa’azi?” inji NUPENG, a martanin da ta yi.

Ta kuma zargi tsohon shugaban NLC da yin kaka-gida wajen cigaba da zama sakatare-janar na ƙungiyar ma’aikatan Atamfa, kayan sawa da ɗinki ta Nijeriya a lokacin da ya zama shugaban NLC.

Sun buga misali da sashe na 31 na ƙungiyar ƙwadago wacce ta ce ta ƙunshi dalilin tafiya yajin aikinsu, tana mai cewa matakin PENGASSAN shi ƙwato wa ma’aikatan da aka sallama daga aikinsu.

By ukarofi