NSA na sane da cin zarafin da wasu ‘yan Nijeriya ke fuskanta wajen jami’an tsaro a filin jiragen sama – Keyamo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce ma’aikatarsa ​​ta kai ƙara ga mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, kan cin zarafin da wasu ‘yan Nijeriya ke fuskanta a hannun wasu jami’an tsaro da ke jibge a filayen tashi da saukar jiragen sama na Nijeriya.

Keyamo, wanda ya kasance baƙo a Gidan Talabijin na Channels Teleɓision a shirin ‘Sunday Politics’ wanda Manhaja ke sa ido a kai, ya ce yana samun rahotanni masu tarin yawa game da rashin ɗa’a na wasu jami’an tsaro a tashoshin jiragen sama.

Ministan ya ce duk da cewa waɗannan ayyuka ba na jami’an ma’aikatar sufurin jiragen sama ba ne, amma ya tuntuɓi hukumar NSA don magance su saboda ya damu da yadda ake muzgunawa fasinjoji.

“Mun kai ƙara ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro saboda mun damu da yadda ake cin zarafin ‘yan Nijeriya. A kula, ba jirgin sama ba ne, ba Keyamo ba ne, ina ganin mutane suna yi mani laƙabi a kodayaushe, ‘wani kawai ya nemi cin hanci daga gare ni’, amma wani ne daga wata hukuma,” in ji Keyamo a cikin shirin.

“Suna yi mani laƙabi a kowane lokaci, ba ni ba ne, ba jirgin sama ba ne. Dole ne mu kai ƙarar ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa wanda ke yin abubuwa da yawa a kan wannan.”

Ministan ya bayyana cewa hukumar ta NSA ta samu kimanin kyamarori 1,000 na jami’an tsaro domin a sa ido sosai kan harkokin filayen jiragen sama.

“Na sha ambata a baya cewa horon ya kusa ƙarewa, ya sayi kyamarori na jiki 1,000 waɗanda duk hukumomin za su saka. Muna so mu fara yin horon farko. Akwai cibiyar umarni don wannan inda kowa zai ga ainihin kyamarori masu motsi a ƙirjin kowa,” in ji shi.

Keyamo ya ƙi amincewa da kiran da aka yi na a janye akasarin jami’an tsaro daga filayen jiragen sama, sai dai ya ce dole ne a sanya ido a kan ayyukansu don ganin sun cika ƙa’idojin da ake buƙata.

Ya yi nuni da kame masu safarar miyagun ƙwayoyi a filayen jiragen sama da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta yi a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ya sa waɗannan hukumomi su kasance a filin jirgin.

“Waɗannan hukumomin su kasance a tashoshin jiragen sama amma su kasance daga gare ku. Ya kamata su kasance a ciki. Idan ka yi zargin wani ne ka fitar da shi ka kai shi wani yanki da aka takaita ka duba mutumin.

“Ba wai duk tsayawa ba sai ka ga NDLEA tana duba jakarka, DSS na duba jakarka da duk wannan–abin da ba mu so ke nan, abin da ‘yan Nijeriya ba sa so ke nan, shi ya sa dole ne mu yi don faranta wa ‘yan Nijeriya rai,” inji shi.