Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyu a sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke jihar, a wani ɓangare na shirin gwamnatin na dasa bishiyu miliyan biyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar a farkon watan Agusta.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, shi ne ya jagoranci kaddamarwar tare da Ko-odinetan NYSC na jiha, inda aka yi taron nuna muhimmancin shuka bishiyoyi a matsayin mataki na kare muhalli da sauyin yanayi.
A cewarsa, masu yi wa ƙasa hidima da aka turo ma’aikatar sun taka muhimmiyar rawa, tare da sabuwar ƙungiyar Climate Change CDS, wadanda suka nuna jajircewa wajen tabbatar da nasarar shirin.
Haka kuma, an ƙaddamar da sabon shirin “Corper ɗaya, Bishiya ɗaya”, wanda zai bai wa fiye da masu yi wa ƙasa hidima 12,000 a jihar damar shiga aikin dads bishiyu, tare da tabbatar da ci gaba da shirin a kowanne sabon rukunin masu yi wa ƙasa hidima.
Ko-odinetan NYSC na jihar ya kuma nemi a kafa gandun itatuwa a sansanin domin kiwon tsirrai da za su tabbatar da dorewar aikin da aka fara.
Dakta Hashim ya bayyana cewa haɗin gwiwar matasa da goyon bayan masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen shuka fata, farfaɗo da tsarin muhalli da kuma gina makoma mai dorewa ga jihar Kano.
