NYSC ta yi barazanar daina tura masu hidimar ƙasa idan ba a ba su masauki ba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yi Wa ƙasa Hidima ta Matasa (NYSC) ta yi barazanar sanya sunayen ma’aikatu da hukumomin da suka gaza samar wa masu hidimar ƙasa masauki da abin hawa cikin jerin waɗanda ba za su ƙara cin gajiyar shirin ba.

Rahotanni sun nuna cewa Darakta Janar na Hukumar NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da masu hidimar ƙasa a Jihar Kogi, a wani ɓangare na ziyarar aiki da ya kai jihar.

An wallafa wannan sanarwa ne a shafukan sada zumunta na NYSC a ranar Talata. A cewar Nafiu, duk wata ma’aikata ko hukuma da ta kasa samar da walwalar da ta dace ga masu hidimar ƙasa da aka tura mata, ba za ta sake samun damar karɓar masu yi wa ƙasa hidima ba.

“Duk wani mai ɗaukar masu hidimar ƙasa da bai samar musu da masauki da kuma abin hawa ba, za a sanya shi cikin jerin waɗanda ba za su ƙara cin gajiyar shirin NYSC ba,” inji shi.

Darakta Janar ɗin ya buƙaci masu ɗaukar masu hidimar ƙasa su ƙara inganta walwalar waɗanda aka tura musu, yana mai cewa hakan zai ƙara musu ƙwazo tare da inganta ayyukan da suke gudanarwa a lokacin hidimarsu.

Ya kuma tabbatar wa masu hidimar ƙasa cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ba da fifiko ga tsaro da walwalarsu.

“Gwamnatin Tarayya ta jajirce wajen tabbatar da tsaro da walwalar ku,” inji Nafiu.

Sai ya yi kira ga gwamnatocin jihohi, na ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara bai wa shirin NYSC cikakken goyon baya. Nafiu ya tunatar da masu hidimar ƙasa cewa tsaro alhakin kowa ne, yana mai ƙarfafa musu gwiwa su kasance masu sa ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro da abin ya shafa.

“Tsaro alhakin kowa ne,” inji shi.

Ya kuma shawarci masu hidimar ƙasa da su kasance masu ladabi, biyayya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu, tare da guje wa duk wani hali da zai iya ɓata sunan hukumar NYSC. Haka kuma, ya buƙace su da su ba da muhimmanci ga Shirin Horar da Sana’o’i da Bunƙasa Kasuwanci, wato Skill Acƙuisition and Entrepreneurship Development (SAED) bayan kammala zaman sansanin horaswa, yana mai bayyana cewa shirin wata babbar dama ce ta dogaro da kai da bunƙasa tattalin arziki.

“Ku kasance masu himma, ku gano damar kasuwanci a al’ummomin da aka tura ku, sannan ku fara samun kuɗin shiga tun daga yanzu,” inji shi.

Da yake magana kan matsin tattalin arzikin da ƙasar ke ciki, Darakta Janar ɗin ya shawarci masu hidimar ƙasa su kasance masu tafiyar da kuɗinsu cikin hikima tare da rungumar al’adar adanawa.

Ya ce, shekarar bautar ƙasa ta zama wata dama da za ta koya musu yadda za su riƙa gudanar da harkokin kuɗinsu yadda ya kamata a nan gaba.

Tun da farko, Kodinetar Hukumar NYSC a Jihar Kogi, Misis Tochi Chika Chris-Moneke, ta yaba wa Darakta Janar kan ziyarar da ya kai jihar, tana mai cewa hakan ya nuna irin kulawar da yake bai wa walwala da tsaron masu hidimar ƙasa da ma’aikatan hukumar. Ta kuma bayyana cewa Sakatariyar NYSC ta Jihar Kogi na shirye-shiryen gudanar da taron horaswa ga ma’aikatun da ke karɓar masu bautar ƙasa, tare da aiwatar da Shirin Kiwon Lafiya ga Mazauna Karkara cikin makonni masu zuwa.

By ukarofi

Leave a Reply