Obasanjo ya yaba wa cibiyar Sasakawa kan gudunmawarta ga noma a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar Sasakawa Africa Association (SAA), Shuichi Suzuki, ya kai ziyarar ban-girma ga tsohon shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, yayin wata mako guda da yake shirin yi a ƙasar domin zurfafa tattaunawa kan rawar da ƙungiyar ke takawa a ci gaban noma da samar da abinci mai ɗorewa.

A ziyarar, Obasanjo ya yaba wa ƙungiyar Sasakawa kan gudunmawarta ga haɓakar harkar noma a Nujeriya da nahiyar Afrika gaba ɗaya. Ya ce shugabannin Afrika ya kamata su yi koyi da irin wannan jajircewa wajen zuba jari a noma, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da jari domin cimma samun nasarorin dogon lokaci a fannin.

A nasa jawabin, Suzuki ya ce ziyarar ta sa ta nufin ƙarfafa haɗin gwiwa da Nijeriya da kuma sake tabbatar da ƙudirin SAA na ci gaba da zuba jari a bangaren noma. Ya bayyana cewa Nijeriya na da manyan dimbin albarkatu — musamman noma da ƙuruciyar al’umma mai yawa — waɗanda su ne ginshiƙan ingantaccen ci gaba na gaba.

A cikin zaman sirri, ɓangarorin biyu sun tattauna hanyoyin da za su ci gaba da tallafa wa manoma ƙanana tare da inganta tsarin noma domin ƙara tabbatar da wadatar abinci da zaman lafiya ta hanyar bunƙasa tattalin arziki.

Daraktan SAA a Nijeriya, Dr. Godwin Atser, wanda ya halarci ziyarar, ya bayyana ta a matsayin mataki mai muhimmanci da zai taimaka wa shugaban ƙungiyar fahimtar ƙalubalen noma a Nijeriya da tasirin da SAA ke samu wajen tallafa wa manoma a sassa daban-daban na ƙasar. Ya ce tun shekaru fiye da ashirin da uku SAA ta riga ta kai ga sama da manoma miliyan ashirin ta hanyoyi daban-daban na horaswa da dabarun bunƙasa samarwa.

Sasakawa Africa Association, wadda aka kafa a 1986, ƙungiya ce mai zaman kanta da ke mayar da hankali kan ilimin gonaki da bunƙasa manoma ƙanana. Hedkwatar ta na Tokyo, tana kuma da ofisoshi a Najeriya, Ethiopia, Mali da Uganda, tun bayan fara aiki a Nijeriya a 1992. ƙungiyar ta yi aiki tare da hukumomin gwamnati, shirye-shiryen raya noma da ƙungiyoyin ci gaba wajen gabatar da fasahohin noma na zamani da tsare-tsaren sauyin yanayi.

Kafin ziyarar Abeokuta, Suzuki ya gana da Jakadan Japan a Nijeriya, Suzuki Hideo; Daraktan Sashen Raya Noma na Tarayya, Olawumi Ayodele; da Daraktar IFAD a Nijeriya, Ms. Dede Ekoue, a Abuja.

Wannan ziyara ita ce ta farko da Mista Suzuki ke kai wa Nijeriya tun bayan karɓar jagorancin SAA, bayan dogon aiki a kamfanin Sumitomo Corporation inda ya riƙe muƙamai na manyan shugabanni a ofisoshi da dama a ƙasashen duniya.

By ukarofi