Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Al’umma sun koka biyo bayan aiwatar da cire N50 kan duk hada-hadar kuɗi da ta kao N10,000 zuwa sama da Opay, Moniepoint da sauran bankunan intanet suka fara a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa ga kwastomomi a ranar Lahadi, 1 ga Disamba, 2024, Moniepoint, ta ce matakin ya bi ƙa’idojin Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS), tare da lura da cewa za a yi amfani da kuɗin ne zuwa asusun sirri da kasuwanci.
Harajin da ake cirewa, wanda ake kira ‘electronic money transfer leɓy’ (EMTL) kuɗi ne da ya kai Naira 50 akan duk wara hada-hadar kuɗi da ta kai Naira 10,000 ko sama da haka zuwa kowane nau’in asusun banki.
A cikin sadarwa daban-daban ga abokan ciniki, Opay ya kuma sanar da aiwatar da haraji daga ranar 1 ga Disamba.
ƙungiyoyi da dama sun nuna rashin amincewa da wannan haraji, ciki har da ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta janye shi.
Kamfanin Opay ya sanar da abokan kasuwancinsa cewa wannan haraji na FIRS ne kuma ba su cin moriyarsa a kowanne fanni.
Bankin ya bayyana cewa; “Ya ku abokin ciniki, daidai da tsarin FIRS, harajin EMTL ya fara aiki daga Disamba 1, 2024.”
Abokan cinikin Palmpay da sauran bankunan intanet sun samu irin wannan sanarwar.