Tallafin fetur: Gwamnatin Tarayya ta fara binciken NNPC kan tiriliyan N2.7

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ofishin Odita-Janar na Tarayya ya karɓi cikakkun takardun da ake buƙata don tantance tallafin man fetur na Naira Tiriliyan 2.7 da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya ya samu gwamnati.

An aiwatar da hakan ne domin sanin haƙiƙanin yadda ake tafiyar kuɗaɗen cire tallafin mai.

Idan dai ba a manta ba, a watan Afrilun 2024, gwamnatin tarayya ta fara wani sabon bincike na neman tallafin man fetur na Naira Tiriliyan 2.8 da hukumar NNPC ta samu.

Wani kamfanin binciken kuɗi mai suna KPMG, ya gudanar da bincike na farko, inda ya rage kuɗin daga tiriliyan N6 zuwa tiriliyan N2.7.

Kamfanin ya ƙara da cewa za a gudanar da binciken ne daga shekarar 2015 zuwa 2021.

A ranar 30 ga Mayu, 2023, ‘yan sa’o’i kaɗan bayan sanarwar “cire tallafin mai” da Shugaba Bola Tinubu ya yi, babban jami’in kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya shaida wa manema labarai na gidan gwamnati cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya na bin kamfanin bashin Naira Tiriliyan 2.8 da aka kashe akan tallafin fetur.

Yayin da yake cewa hukumar NNPC ta kafa kuɗazen tallafin man fetur daga kudaden da take yi, Kyari ya ce kawo yanzu gwamnati ta kasa biyan tiriliyan tiriliyan N2.8.

Ya ce, “Tun da aka samar da tiriliyan N6 a shekarar 2022 da kuma tiriliyan N3.7 a shekarar 2023, ba mu samu komai daga Tarayya ba.

“Hakan na nufin su (Gwamnatin Tarayya) ba za su iya biya ba kuma mun ci gaba da tallafa wa wannan tallafi daga kuɗaɗen da ake samu a NNPC. Muna jiran su daidaita har tirliyan N2.8 na kuɗaɗen da NNPC ke samu daga tsarin tallafin kuma ba za mu iya ci gaba da gina wannan ba.

Da yake ba da ƙarin bayani a cikin mintuna na taron kwamitin kasafin kuɗi na tarayya na watan Satumba na 2024, Daraktan Kuɗi na Gida, Ali Mohammed, ya ce za a gudanar da aikin cikin adalci.