Majalisar Wakilai ta fara binciken yi wa ma’aikatan CBN ritaya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Wakilai ta yanke shawarar kafa wani kwamitin wucin gadi na musamman da nufin binciken zargin yi wa ma’aikatan Babban Bankin Nijeriya 1,000 ritaya.

Haka kuma ana sa ran kwamitin zai binciki shirin biyan Naira biliyan 50 da aka ruwaito ga ma’aikatan da abin ya shafa domin tantance gaskiya da riƙon amana da kuma amfani da kuɗaɗe yadda ya kamata, tare da gudanar da jagorancin babban bankin na CBN domin tantance irin tasirin da zai iya haifarwa a kan tattalin arziki a fannin hada-hadar kuɗi a Nijeriya, inda zai ba da rahoto cikin makonni huɗu.

A halin da ake ciki, an buƙaci CBN da ya dakatar da ci gaba da aiwatar da shirin yi wa ma’aikata ritaya da kuma tsarin biyan albashi mai alaƙa da shi har sai an kammala binciken majalisar, kamar yadda majalisar ta yi kira ga ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya da ta tabbatar da haƙƙin waɗanda abin ya shafa kamar yadda dokokin kwadagon Nijeriya suka tanada.

Kudurin a ranar Talata, ya biyo bayan ƙudirin da Hon. Kama Nkemkama, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ohaozara/Oncha/Iɓo na jihar Ebonyi akan “Buƙatar Bincika Ma’aikatan Babban Bankin Nijeriya (CBN) sama da 1,000 da suka yi ritaya da kuma shirin biyan biliyan N50”.

Dan majalisar ya ce, akwai wani shiri da ake zargin babban bankin na gudanar da aikin “a wani ɓangare na sake fasalinsa a karkashin jagorancin Muƙaddashin Gwamna,” inda ya kara da cewa an shirya shirin biyan kuɗi naira biliyan 50 don biyan ma’aikatan da abin ya shafa, a matsayin wani ɓangare na rufe musu baki, tare da ikirarin cewa tsarin zai tabbatar da daidaito”.