
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan wasan gaba na Super Eagles ta Nijeriya, Victor Osimhen, ya sake nuna bajinta bayan da ya zura ƙwallo biyu a wasan da ƙungiyarsa Galatasaray ta doke Antalyaspor da ci 4-2, lamarin da ya tabbatar wa ƙungiyar lashe kofin gasar Turkish Super Lig karo na huɗu a jere.
Nasarar ta sa Galatasaray ta lashe kofin gasar Turkiyya karo na 26 a tarihinta, wanda ya ƙara tabbatar da ita a matsayin ƙungiyar da ta fi kowacce nasara a Turkiyya.
Osimhen ya kasance cikin fitattun ’yan wasan ƙungiyar tun bayan komawarsa daga Napoli ta ƙasar Italiya, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori a karkar wasan bana.
Rahotanni sun ce manyan ƙungiyoyin Turai na cigaba da bibiyar tauraron ɗan wasan gabanin buɗe kasuwar cinikayyar ’yan wasa ta bazara.
