Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta soke ‘yan takarar ɓangaren Fubara, ta tantance 33 a zaɓen majalisa na fidda gwani

Spread the love

Kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC ya hana tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Ribas na tsagi Hon. Victor Oko Jumbo da wasu ‘yan takara 64 shiga zaɓen fidda gwani na majalisar dokokin jihar gabanin zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa, galibin waɗanda aka hana tsayawa takarar na daga cikin magoya bayan gwamnan jihar Siminalayi Fubara ne.

Rahoton kwamitin tantancewar, wanda shugaban kwamitin Rt. Hon. Muraina Ajibola da wasu mambobi uku suka sanya wa hannu, ya bayyana cewa an cire ‘yan takarar ne saboda rashin cika wasu sharuddan jam’iyya.

Sai dai kwamitin ya amince da ƴan takara 33 da ake alaƙanta su da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, domin shiga zaɓen fidda gwani.

Yawancin waɗanda aka tantance ɗin mambobin majalisar dokokin jihar Rivers ne masu ci a yanzu.

Lamarin ya ƙara tayar da ƙura a siyasar jihar Rivers, inda ake ganin rikicin siyasa tsakanin ɓangaren Wike da na Fubara na ci gaba da ƙamari gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Wani daga cikin magoya bayan Fubara ya bayyana cewa matakin da APC ta ɗauka na iya jawo wa jam’iyyar matsala a zaɓe mai zuwa, yana mai cewa cire manyan masu ruwa da tsaki daga cikin jam’iyyar na iya raunana ƙarfinta a jihar.

By Babaji