Soja ya bindige maigadin otel a Keffi

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Wani jami’in tsaro da ke aiki a Princess Sarah Hotel da ke Keffi a jihar Nasarawa da ba a bayyana sunarsa ba an harbe shi da bindiga har lahira yayin wani rashin jituwa da ya auku tsakanin sa da wani soja da ke aiki a baraki na 177 Guards Battalion dake birnin Keffi ƙarƙashin Operation MESA.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:40 na safe ranar Asabar 2026 lokacin da dakarun sojan dake sintiri na musamman suka cikaro da saɓani tsakanin shi marigayi maigadin otal ɗin da wani mai babur na haya.

A cewar majiyoyin jami’in tsaron dake aiki a hotel na Princess Sarah din wanda ake cewa tsohon soja ne da aka kore shi daga aiki kamin daga bisani ya samu aiki da hotel ɗin ya tsare mai babur ɗin ne inda nan take gardama ta taso tsakanin su kafin tawagar sintirin ta iso wurin.

Matsala ta fara ne bayan ɗaya daga cikin sojojin ya yi ƙoƙarin shiga tsakani domin taimakon mai babur ɗin da ya lura kamar maigadin yafi ƙarfin sa.

Yayin kace-nacen ne sai maigadin ya fara zargi tare da dukan sojan shima sannan yayi yunƙurin ƙwace bindigarsa wanda hakan ya haifar da arangama tsakanin su biyun kuma.

Majiyoyin sun ce daganan ne sai sojan nan take ya danna kunamar bindigar tasa ya harbi jami’in tsaron sannan daga bisani aka garzaya da shi asibitin Federal Medical Centre da ke nan Keffi domin duba lafiyarsa inda daga baya yace ga garinku.

Sai dai koda yake a nasa ɓangaren mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Nasararsa SP Rahman Nansel yace zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto bai samu labarin aukuwar mummunar lamarin ko ba. Amma a cewarsa jami’ansu tabbas za su gudanar da cikakken bincike don gano wannan labarin da kuma yadda lamarin ya faru idan da gaskiya ne ya farun.

By ukarofi