Barcelona ta lashe kofin Laliga na 29 bayan doke Real Madrid

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta tabbatar da lashe kofin LaLiga karo na 29 bayan doke Real Madrid da ci 2 da 0 a wasan El Clasico na ranar Lahadi.

Tuni dai yaran Hansi Flick suka shiga wasan da tazarar maki 11 tsakaninsu da abokan hamayyarsu, Real Madrid da ke matsayi na biyu.

Barcelona ta mamaye wasan ne tun a farkon lokaci a Camp Nou, inda Marcus Rashford ya fara zura kwallo ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, kafin Ferran Torres ya ƙara ta biyu.

Duk da ƙoƙarin da Madrid ta yi na dawowa a karo na biyu, ba a sake samun ƙwallo ba har aka kammala wasan.

Wannan sakamako ya nuna Barcelona ta kai maki 91, yayin da Alvaro Arbeloa na Madrid yake a maki 77, abin da ya tabbatar da cewa ba za su iya kamo abokiyar hamayya tasu ba.

Wannan shi karo na uku a jere da Barcelona ke lashe kofin, lamarin da ke nuna ta cigaba da kare kambenta.

By Babaji