‘Yan bindiga 70 harin sojoji ya halaka a Neja, ba fararen hula ba, inji Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Hedikwatar Tsaro DHQ, ta musanta rahotannin da ke cewa an halaka fararen hula a yayin hare-haren sama da rundunar soji ta kai a Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, inda ta ce, an kai su ne akan maboyar ’yan bindiga.

Daraktan Yaɗa Labaran Harkokin Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, rundunar soji ta kai hare haren ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ’yan bindiga sun taru a ƙauyen Lukupe a ranar 9 ga Mayun 2026.

Ta ce, rundunar jiragen yaƙi marasa matuƙa ta soji sun kai hare-hare tsakanin ƙarfe 11:59 na dare zuwa ƙarfe 6 na safe a ƙauyukan Katerma da Bokko da Kusasu da Kuduru.

Manjo Janar Onoja ya ce bayanan da aka samu daga yankin sun tabbatar da cewa hare-haren sun kai inda aka nufa, inda aka kashe kimanin ’yan bindiga 70 a ƙauyen Kusasu kaɗai.

Hedikwatar tsaron ta ƙara da cewa an hangi wasu ɗaruruwan ’yan bindiga a kan babura suna yunƙurin haɗuwa domin kai sababbin hare-hare a wasu yankuna, lamarin da ya sa sojoji suka ɗauki matakin gaggawa.

Sai dai rundunar ta ce ta umarci jami’anta su binciki duk wani zargin cewa an samu asarar rayukan fararen hula. Haka kuma ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da jama’a su guji yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da su ba domin kada su kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro.

By Babaji