An yi walimar goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kano na ADC, Sheikh Ibrahim Khalil

Spread the love

An gudanar da wani gagarumin biki da Kungiyoyin Khalil suka shirya domin nuna goyon baya ga dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Malam Ibrahim Khalil, inda jama’a da dama daga sassa daban-daban suka halarta.

Taron ya samu halartar farfesoshi, malamai addinin Musulunci, wakilan Kiristoci, mata, matasa da sauran magoya baya da suka taru domin nuna goyon baya ga takarar Malam Ibrahim Khalil gabanin zaben da ke tafe.

A yayin taron, masu jawabi da dama sun bayyana damuwa kan halin da jihar Kano da Najeriya baki daya ke ciki. Yawancinsu sun bayyana cewa jam’iyyar ADC ita ce mafita ga matsalolin siyasa da tattalin arzikin kasar nan, tare da kira ga jama’a da su mara wa jam’iyyar baya domin samun sauyi mai anfani.

Masu jawabin sun kuma bukaci al’umma da su tabbatar sun mallaki katin zabensu na dindindin (PVC) tare da shirya fitowa zabe domin kada kuri’unsu ga jam’iyyar ADC a lokacin zabe.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, dan takarar gwamnan Kano na ADC, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa shiga siyasarsa ba domin son rai ko anfani na kai ba ne, sai domin kare muradun talakawa da magance matsalolin da suke fuskanta.

Ya ce da ace talakawa na rayuwa cikin walwala ba tare da wahala da rashin adalci ba, da bai shiga siyasa ba. Amma muddin matsalolin al’umma ba su warware ba, shi da magoya bayansa za su ci gaba da fafutukar ganin an samar da adalci, daidaito da rayuwa mai kyau ga kowa a jihar Kano.

Malam Ibrahim Khalil ya kuma jaddada muhimmancin shugabanci nagari wanda zai kare hakkokin kowane dan kasa ba tare da nuna bambanci ba, yana mai tabbatar da cewa idan aka ba shi dama zai mayar da hankali wajen samar da ci gaba da walwalar jama’a.

Shi ma da yake nasa jawabin, wani wakili daga bangaren Kiristoci ya bayyana cewa suna da yakinin Malam Ibrahim Khalil zai samar da shugabanci na gari da gyara a jihar Kano.

Wakilin ya bayyana cewa shi da sauran mabiya addinin Kirista za su kada kuri’unsu ga Malam Ibrahim Khalil, tare da kira ga daukacin Kiristocin jihar Kano da su fito su yi amfani da hakkinsu na zabe wajen goyon bayan dan takarar ADC.

An kammala taron da kira ga hadin kai, zaman lafiya da kuma shiga harkokin siyasa cikin lumana domin gina Kano da Najeriya mai inganci ga kowa.

By Babaji