Osinbanjo ya bayyana wa Buhari aniyarsa ta tsayawa takara 2023

Daga SANI AHMAD GIWA

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya sanar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari shirinsa na neman kujerar shugabancin ƙasar a zaven 2023.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa bayan wata da watanni ana raɗe-raɗi, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa yana sha’awar shugabancin ƙasa.

Farfesa Yemi Osinbajo ya faɗa wa mai gidansa cewa idan so samu ne, ya karvi ragamar shugabancin ƙasar nan daga hannunsa a Mayun 2023.

Osinbajo yana ganin hakan zai bada damar cigaba da samun nasarorin da aka gani daga lokacin da gwamnatin APC ta karɓi mulki a hannun jam’iyyar PDP.

Jaridar Daily Trust ta ce har zuwa yau, mataimakin shugaban ƙasar Nijeriyar bai sanar da duniya game da burinsa na tsayawa takara a zaɓe mai zuwa ba.

Sai dai wata majiya daga fadar Villa ta shaida cewa, “shakka babu, mataimakin shugaban ƙasa Osinbajo ya faɗa wa shugaban ƙasa cewa yana so ya gaje shi.

“Mataimakin shugaban ƙasar ya fara tuntuvar wasu manyan ƙasa, waɗanda suka ba shi ƙwarin gwiwa, suka ƙarfafa masa baya ya nemi mulki.

“Daga nan suka ba shi shawarar ya faɗa wa shugaban qasa da kan shi. Sun faɗa masa cewa ka da ya bari wasu su faɗa wa Buharin a madadinsa.”

Wata majiyar kuma ta shaida wa jaridar cewa da Osinbajo ya kai wa Buhari maganar, kamar yadda ya saba, sai ya yi murmushi kurum yana sauraron abin da yake faɗa.

Majiyar ta ce, Shugaba Buhari ya nuna wa Osinbajo cewa zai iya jarraba sa’arsa, amma bai tabbatar masa da cewa zai mara masa baya a kan sauran ‘yan takara ba.

Haka shugaban ƙasar ya yi a lokacin da Bola Tinubu ya zauna da shi a fadar Aso Villa, bai nuna masa ya janye takara ba, bai kuma ce yana tare da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *