Pakistan ga Turai: Mu ba bayinku ba ne da za ku ce sai mun yi tir da Rasha

Firaministan Ƙasar Pakistan, Imran Khan, ya yi allawadai da umarnin da da ƙasashen Yamacin Duniya (Turai da Amurka da sauransu) suke yi wa ƙasar Pakistan da su fito su yi tofin Allah tsine ga ƙasar Rasha saboda saɓaninta da ƙasar Yukiren.

Inda Imran Khan ya mayar wa Gamayyar ƙasashen Turai (EU) martani cewa, ko tana tsammanin cewa, Pakistan baiwarta ce, da take ba ta umarni ta yanke hulɗa da ƙasar Rasha saboda rikicinta da Yukiren?

A cikin wani rubutaccen saƙo na haɗin gwiwa da Ƙasashen Yammacin Duniya suka aike wa da Ƙasar Pakistan a farkon watan nan na Maris 2022, an ba da Umarni ga ƙasar Musuluncin ta Pakistan da ta fito sarari ta yi bara’a da Moscow wato babban birnin ƙasar Rasha. 

Jaridar Reuters ta rawaito yadda Firayim ministan ya mai da martani ga rasha: Imran Khan ya ce: “Me kuka ɗauke mu ne? Mu bayinku ne….da dukkan abinda kuka umarce mu tilas mu aikata shi?

Wannan cece-ku cen ya samo asali ne bayan ziyarar da Firayi Minista Khan ya kai wa Vladimir Putin na ƙasar Rasha a ƙarshen watan da ya gabata da nufin Safarar gas da alkama daga Rasha zuwa ƙasar Pakistan.