PDP a Jihar Benue ta dakatar da Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Ayu saboda zagon ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA

Rikicin cikin gidan jam’iyyar adawa ta PDP na cigaba da zafafa, yayin da Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov da ke ƙaramar hukumar Gboko ta Jihar Benue ya dakatar da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa Iyorchia Ayu nan take.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa sun dakatar da Ayu ne saboda nuna adawa da jam’iyyar bayan sun kaɗa masa ƙuri’a.

A lokacin da yake karanta wani ƙudiri, Sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Banger Dooyum, ya ce zagon ƙasa da Ayu tare da abokansa suka yi wa jam’iyyar ya taimaka wajen rashin yin nasarar Jam’iyyar PDP a mazaɓarsa da ƙaramar hukumarsa a zaɓen gwamna.

Ana kuma zargin Ayu da rashin biyansa kuɗaɗen shekara kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada. Sha biyu daga cikin exco goma sha bakwai sun rattaɓa hannu a kan takardun da ke tabbatar da dakatar da shi.

Sun kuma yi zargin cewa jigon PDP bai kaɗa ƙuri’a ba a lokacin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

A cewarsu, yawancin makusantan Ayu sun yi aiki ne da jam’iyyar adawa ta All Progressive Congress (APC) wanda hakan ya haifar da mummunan aiki na PDP a Igyorov Ward.

Shugaban gundumar Igyorov, Kashi Philip, shi ma ya sanya hannu kan wasiƙar tare da ‘exco’.