Sanata Lawan ya ‘yanta fursunoni 15 a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Sakamakon alfarmar watan Ramadan, Shugaban Majisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya biya wa fursunoni 15 bashi a gidan gyaran hali da ke garin Gashu’a, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe.

Waɗanda suka ci gajiyar afuwar sun haɗa da mutum huɗu daga ƙaramar hukumar Yusufari, uku daga Jakosko, yayin da sauran suka fito daga Potiskum da Bursari duk a jihar Yobe.

Bayan haka, Sanata Lawan ya bai wa kowannensu kyautar Naira 50,000 da yadin shadda 10 domin su koma cikin iyalinsu tare da gudanar da ayyukan ibadar watan Ramadan.

Da yake jawabi a madadin Shugaban Majisar Dattawan, Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Ibrahim Babagana, ya ce sun gudanar da wannan aikin jinƙan ne bisa umurnin Sanata Ahmed Lawan, a matsayin jinƙai ga waɗanda lamarin ya shafa waɗan aka yanke musu zaman gidan kaso sakamakon bashin da ake binsu.

“Duk da ba iya adadin da ya ba mu umurnin a yi wa afuwar ba ke nan, ya ce mu biya wa waɗanda ake bi bashin, amma sauran laifukan ba zai tsoma baki a ciki ba. Al’amarin da ya jawo wannan adadi na mutum 15 ne kaɗai muka samu a nan gidan gyaran hali da ke Gashu’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Aƙalla ya kashe sama da naira miliyan uku wajen ‘yanto waɗannan mutanen, kuma ya tallafa wa kowane mutum ɗaya da kyautar Naira 50,000 da yadin shadda 10. Muna yi masa addu’ar Allah ya saka masa da alheri.”

Tuni dai waɗannan mutane suka kama hanyar komawa cikin iyalinsu, tare da bayyana farinciki da godiya ga Sanata Lawan.

Sun kuma yi masa addu’ar Allah ya cika masa burinsa bisa ga faranta musu da ya yi a daidai wannan lokaci na watan Ramadan mai tsarki.