Kotu ta hana Iyorchia Ayu ci gaba da bayyana kansa a matsayin Shugaban PDP

*NEC kaɗai ke da ikon dakatar da ni – Ayu

Daga BASHIR ISAH

Wata Babbar Kotu mai zamanta a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai, ta hana wa Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu, ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Alƙalin kotun, W.I. Kpochi, shi ne ya ba da wannan umarni ranar Litinin biyo bayan ƙarar da Conrad Terhide Utaan ya shigar mai lamba MHC/633/2023.

Daga nan, kotu ta ɗage ci gaba da sauraren ƙarar zuwa ranar 17 ga Afrilun 2023.

A hannu guda, Iyorchia Ayu ya ce shugabancin PDP a matakin ƙasa (NEC) kaɗai ke da ikon dakatar da shi kamar yadda dokar jam’iyyar ta tanada, amma ba wani ba.

Ya ƙara da cewa, sanarwar dakatar da shi ba komai ba ne face aikin masharranta da farfaganda.

Ya ce abu ne da aka tsara shi cikin “jahilci da kuma neman a ci da zafi”.

Yanzu dai abin jira a gani, shi ne yadda zaman kotun zai kasance kan batun ya zuwa ranar 17 ga Afrilu idan Allah Ya kai mu.