PDP ta ɗage taron kwamitin zartarwarta don bai wa gwamnoni yin matsaya kan Damagum

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar PDP za ta ɗage taronta na Kwamitin Zartarwa na ƙasa da aka shirya gudanarwa tun da farko a ranar 24 ga watan Oktoba domin bai wa gwamnoni damar cimma matsaya kan hanyoyin siyasa don sauƙaƙa ficewar shugaban riƙo na ƙasa Umar Damagum daga jam’iyyar.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na NWC da dama, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana a kan batun, sun bayyana cewa za a jinkirta taron kwamitin ne saboda gwamnonin da ke ƙoƙarin ganin an shawo kan rikicin na baya-bayan nan da kuma ba da lokaci don magance matsalolin da ke kawo cikas ga cigaba jam’iyyar.

Idan dai za a iya tunawa, tun bayan da aka tsige Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar PDP na ƙasa bayan umarnin, Damagum na fuskantar ƙarin suka daga shugabannin jam’iyyar a cikin rikicin da ke faruwa na cikin gida, lamarin da ya sa ake kira da ya yi murabus.

Rashin ɗaukar matakin ya ƙara dagula al’amura a Jihar Ribas, musamman tsakanin Gwamna Siminalaye Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

A wani al’amari mai ban mamaki a ranar Juma’a, ɓangaren Damagum na NWC ya sanar da dakatar da sakataren yaɗa labarai na ƙasa Debo Ologunagba da kuma mai ba shugaban shawara kan harkokin shari’a Kamaldeen Ajibade (SAN) bisa zargin cin zarafi da ayyukan da suka yi na cutar da jam’iyyar.

Jim kaɗan bayan haka, Ologunagba ya mayar da martani inda ya bayyana cewa kwamitin ta NWC ta dakatar da Damagum da sakataren ƙasa Sen. Samuel Anyanwu saboda rashin biyayya, inda ya naɗa ma’ajin ƙasa Yayari Ahmed Mohammed a matsayin shugaban riƙo na ƙasa.

Sai dai a ranar Talata, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa an warware rigingimun cikin gida, an ɗage dakatarwar da aka yi, inda ya ƙara da cewa NWC ta koma matsayin da take a ƙarƙashin Damagum.

By ukarofi