PDP ta dakatar da Sanata Umar Tsauri a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jam’iyyar PDP a gundumar Tsauri a ƙaramar hukumar Kurfi da ke Jihar Katsina, ta dakatar da tsohon Sakatarenta na ƙasa, Umar Ibrahim Tsauri.

A wata takarda da ke ɗauke da sa hannun shugaba da sakataren na jam’iyyar, Danjuma Abubakar da Abdullahi Garba suka aika sa zuwa ga shugaban jam’iyyar ta jiha, sun dakatar da Sanata Tsauri ne bisa yi wa jam’iyyar zangon-ƙasa .

Haka kuma, jam’iyyar ta zarge shi da maganganu na tayar da husuma ga shugabanninta na ƙasa da kuma nuna halayya da mu’amullar da ka iya haifar da ruɗani a jam’iyyar.

Sun ce, sun ɗauki wannan mataki ne a ƙarƙashin sashe na 59(1) na kundin tsarin mulkin Jam’iyyar.

Sakataren yaɗa labarai na PDP reshen jihar, Lawal Audi Yar’Adua ya tabbatar da sanarwar dakatarwar da akayi wa tsohon Sakataren.

Ya ƙara da cewa, tuni uwar jam’iyyar ta kafa kwamitin mutum uku da zai binciko zargin da ake yi wa Sanata tsauri.

Kwamitin zai gayyato Sanatan ya gurfana a gabansa domin ya wanke laifinsa wanda idan ba a same shi da laifin ba, to shikenan an wanke shi, yayin da idan kuma kwamitin ya same shi da laifin to zai fuskanci hukunci dai-dai da laifin da ya aikata.

Da yake mayar da martani game da takardar dakatarwar, Tsauri ya ce, kawo yanzu bai ga takardar dakatarwar ba balle ya ɗauki mataki a kai.

Sanata Tsauri, wanda ya gana da manema labarai ta wayar tarho, ya ce ba wai jami’ya a matakin gunduma ba, ko a matakin jiha ne, ba su da hurumin dakatar da shi.

By Babaji