PDP ta tsayar da Sandy Onor takarar shugaban ƙasa a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsagin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike da Abdurrahman Mohammed ya ayyana tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Sandy Onor, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a Zaɓen 2027 bayan masalahar da aka gudanar.

Tsohon gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, wanda shi ne shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani, ya sanar da hakan yayin tattara sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar Talata a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.

Kwamitin zaɓen ya ce an gudanar da zaɓen ne ta hanyar tuntuɓa da kuma masalahar goyon baya daga mambobin jam’iyyar a jihohin ƙasar nan.

Sanata Onor ya samu tikitin ne bayan ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP tare da sayen fom ɗin takara kamar yadda dokokin jam’iyyar suka tanada.

By ukarofi

Leave a Reply