Pele ya yi bankwana da iyalansa akan gadon asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An ga fitaccen ɗan wasan ƙasar Brazil, Pele, yana bankwana da iyalansa da abokan arziki daga gadon asibiti a cikin wani faifen bidiyo.

Yanayin jikin zakaran wasan ƙwallon ƙafar duniya, wanda da ya ɗauki kofin zama zakara sau uku ya tayar da hankali. Bidiyon ya nuna shi yana faman numfashi da ƙyar.

Ɗan shekaru 82, wanda aka cire masa wata cuta daga hanjinsa a watan Satumbar 2021, an kwantar da shi a Asibitin Isra’ila Albert Einstein a Sao Paulo a ranar 29 ga Nuwamba, 2022.

Ya kasance a asibiti har ranar Kirsimeti tare da masoyansa a gefensa. ‘Yarsa ta sha alwashin cewa za ta kasance a wurinsa yayin da yake samun kulawa a asibiti bayan ciwon daji da ake fama da ita.

A cikin faifan bidiyo na baya-bayan nan da ke yaɗuwa, an ga Pele kewaye da wasu mata biyu waɗanda suka riƙe masa waya a gabansa yayin da yake isar da saƙo.

Wani ɗan kasuwa kuma manajan wasanni na Burtaniya, Frank Khalid ya rubuta a shafin Tiwita cewa, “Pele ya yi bankwana da dangi da abokai daga gadon asibiti. Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa, Pele sannu a hankali cutar dajin na ƙara cin jikinsa, inda danginsa da ‘yanayinsa ke cewa yana ƙara ta’azzara.”