‘Yan siyasa ke maguɗin zaɓe ba mu ba, inji INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ba za ta bari a yi maguɗin zaɓe a babban zaɓe mai zuwa na 2023 ba, domin daman ba halinta ba ne.

Sabuwar Kwamishinar Zaɓe ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi ce ta bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula, CSOs.

A cewarta, maguɗin zaɓe zai yi matuqar wahala domin hukumar ta shirya tsaf domin tabbatar da sahihin zae.

Misis Ugochi ta ce: “INEC ba za ta taɓa yin maguɗin zaɓe ba. ‘Yan siyasa ne ke tafka maguɗin zaɓe. Za mu yi iya gwargwadon abin da za mu iya wajen daƙile maguɗin zaɓe.

“Tsarin yanzu ya sanya maguɗin zave ya na da matuqar wahala. Idan kuna son yin maguɗi a yanzu muna da BVAS. Shin ta hanyar satar hanya ta BVAS ne ko kuma kulle rumbun ajiye bayanai nan jiɓaɓɓen abin mu na tsakiya inda komai yake?

“Yanzu yana da wahala sosai. Wannan lokaci ne da kafafen yaɗa labarai da CSOs za su yi aiki tuƙuru da kuma wayar da kan jama’a. Mu ba ma nuƙu-nuƙu za mu yi iya ƙoƙarinmu a duk abin da muke yi.

“Za mu tsaya tsayin daka domin tare duk wani hari daga waje. Ya kamata kafafen yaɗa labarai su ba mu goyon baya don ka da mu samu matsaloli a abin da muka sa a gaba,” inji ta.