Jiragen ruwa maƙare da man fetur sun maƙale a kan teku ana tsaka da ƙarancin mai a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ake tsaka da ƙaranci da tsadar man fetur da ya ƙi ci, ya qi cinyewa a Nijeriya, a yanzu haka jiragen ruwa waɗanda suke maqare da man fetur, gas, baƙin mai da man jirgin sama suna nan suna jiran sahalewar dakarun tashar jirgin ruwan Legas don sauke kayansu.

Duk kuwa da tsada da ƙarancin man fetur da ake ciki a ƙasar da ta kai ga ana sayar da man fetur daga Naira 170 yanzu ya koma 260 kowacce lita a gidajen mai, wasu gidajen ma an garwaye su saboda babu ma man da za su sayar.

Sakamakon binciken da Hukumar kula da tashoshin Nijeriya ta NPA da jaridar Ingilishi ta The Guardian ta rawaito, ta bayyana cewa, jiragen masu sunaye More West, Rich Harvest, Proodos, Flagship Sage, Stena Imprimis, Super Ruby, Alfred Temile, Laperouse, da kuma Maestro har yanzu suna nan suna jiran a tashar jirgin ruwa, kuma har yanzu jami’an hana fasa ƙwauri na Nijeriya wato Kwastan ba su ba su izinin ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, jinkirin ba ya rasa nasaba da da yanayin gudanar da aikin Kwastan (NCS) ɗin da dogayen sharuɗɗan da cike-ciken takardu.

Kodayake har yanzu ana fuskantar dogayen layukan shan mai a gidajen man, dillalan man fetur masu zaman kansu suna ta miƙa koken su ga gwamnati musamman kamfanin rarraba man fetur na NNPC a kan a sakar musu kaya, kuma a ba su shi a kan farashin mai kyau.

Hakazalika, kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na gida Nijeriya a ƙarƙashin ƙungiyar ta (AON) su ma a ta bakin kakakinsu, Obiora Okonkwo, sun yi jan kunne ga gwamnatin da cewa ƙarancin man jirgin zai iya jawo cikas ga harkar sufurin jiragen saman. Wato kamar yadda ya jawo tsaiki da matsaloli a yayin sufurin mutane a lokacin bikin Kirismeti.