Malamai a Bauchi sun ƙalubalanci hukuncin kisa a kan Abduljabbar

• Sun ce za su ɗaukaka ƙara

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Wasu Jiga-jigan malaman addinin Musulunci dake ƙarƙashin tutar ‘As’habul Kahfi Warraqeen’ mazauna garin Bauchi sun yi kakkausar suka da fatali da abinda suka kira saɓanin addinin Islama, da hukunci kisa na jeka-na-yika da Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya zartar a kan Shehin Malami Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin yin ɓatanci ga Shugaban Halitta Muhammadu, (SAW) Aminci Allah ya tabbata a gare shi.

“Wannan banbaraqwai da Islama, jeka-na-yi-kan hukunci da Ibrahim Sarki Yola ya zargi ɗumgurugum ɗinsa ba daidai ba ne kuma baya cikin Islama, saboda haka mun yi fatali da shi, domin hukuncin tun daga farko har ƙarshen sa an gudanar da shi ne baibai, a cewar jami’i mai magana da yawun waɗannan malamai, Abdullahi Musa.

Jami’in sadarwar na tutar ‘As’habul Kahfi Warraqeen’ ya faɗi a cikin wani rubutaccen jawabi da ya rabawa manema labarai a garin Bauchi a ranar Litinin da ta gabata cewar, hukuncin yana maƙare da siyasar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, domin Shehi Abduljabbar ya kasance mai yin suka ne wa Gwamna Ganduje ta cin hanci da rashawa, waɗanda shi Abduljabbar yake adawa da su.

“Mun fahimci cewar, wasu ‘ya’yan ɗariku sun taru sun yi wani gungu da zummar shafe Abduljabbar daga doron ƙasa, kuma sune suka duƙufa wajen aibunta Ma’aiki a cikin koyarwar su daban-daban, kuma babu wani maluqi da ya tuhumci katoɓara da suke yi, kamar yadda suka ci gaba da wanzar da faɗakarwar addin.”

Malam Abdullahi Musa ya zayyana sunayen waɗanda yake gani suna yin ɓatanci wa Manzon Tsira (SAW) kamar haka: “Ƙaribullah Kabara, Abdulrazak Yahya Haifan, Abbas Jega, Jalo Jalingo, Ahmad Gumi, Abdulwahab Abdullah da Sani Rijiyar Lemo, yana mai cewar “amma saboda alaƙar su da mahukunta, babu wanda ya tuhumce su, yayin da shugaban mu na ruhaniya yake ta samun aibuntawa.

“Da farko dai, ba mu gamsu da hukuncin ba, domin muna da yaƙinin akwai sanya bakin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, haɗi da wasu malamai dake cikin jihar waɗanda ba su jituwa da Abduljabbar na tsawon lokaci dake tafe.

“Sun yi haɗin baki akan sa, tare da yi masa ƙazafin yin ɓatanci ga shugaban halitta, domin su shafa masa laifi da zummar shafe shi daga doron ƙasa ta hanyar yin amfani da kotu,” a cewar jami’in sadarwa Abdullahi Musa.

Kamar yadda ya ce, zargi ko ƙagen yi wa Shehi Abduljabbar yin vatanci ga shugaban halitta ba komai ba ne face shelar ɓatancin hali da baƙantawa da abokan adawa sukeyi masa, har da Gwamna Ganduje, haɗi da wasu shehunai da farin jinin Abduljabbar ya kasance barazana a garesu.

Malam Abdullahi Musa ya kuma bayyana cewar, waɗancan abokan adawa sune suka yi wa Abduljabbar qagen ɓatanci domin su ɓata masa suna, kuma suka yi gum a kan aniyarsu ta shafe rayuwarsa, kuma bisa wannan nufaqa ce ya sa waɗannan malamai dake garin Bauchi za su ɗaukaka ƙara zuwa mafi girman kotu da zummar yin fatali da wancan hukunci, haɗi wanzar masa ‘yanci.

Musa ya ce ta hanyar ɗaukaka ƙara zuwa kotun sama, waɗannan shehunai na garin Bauchi za su dawo wa da Shehi Abduljabbar haƙƙoƙinsa, musamman ‘yancin gudanar da addini da ra’ayi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Ya ce, malaman na garin Bauchi suna yin kira ga Hukumar Wanzar da ‘Yanci (HRC), Ƙungiyar Samar da Afuwa ta Ƙasa da Ƙasa, wasu hukumomin wanzar da ‘yanci na ƙasa dana ƙetare, haɗi da lauyoyin fafutukar ‘yanci kamar Femi Falana, masu fafutukar neman ‘yanci kamar Ahmad Isa da sauransu, su shigo cikin wannan fafutuka na yin fatali da rashin adalci, haɗi da yin watsi da haɗin bakin masu adawa ta hanyar taimakon shara’ar bin ƙa’ida na adalci.